Gwamnan Kano zai biya wa daliban BUK 7,000 kudin makaranta
Tallafin zai shafi dalibai ’yan asalin Jihar da ke karatu a jami’ar
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin biya wa daliban da ke karatu a Jami’ar Bayero (BUK) kimanin su 7,000 ’yan asalin Jihar kudin makaranta.
Babban mai taimaka wa Gwamnan a kan harkokin kafafen sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro, ne ya tabbatar da haka a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da maraicen Laraba.
- KAROTA ta kama mutum 3 kan zargin buga takardun bogi a Kano
- An kama tsohon shekara 94 kan zargin yi wa yarinya fyade
“Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin biya wa ɗaliban jihar Kano da ke karatu a BUK su kimanin dubu bakwai kuɗin makaranta,” kamar yadda ya wallafa.
Hakan na zuwa ne dai a daidai lokacin da daliban jami’ar ke ci gaba da kokawa da karin kudin da jami’ar ta yi.
A sakamakon karin, dalibai da dama sun rika neman gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa musu.
Hatta jami’ar ta Bayero sai da ta tsawaita wa’adin lokacin yin rajistar dalibai, kasancewar da dama daga cikinsu ba su iya kammalawa ba, saboda tsadar.