Gwamnan Kano zai mayar da ginin shataletalen da ya rusa

Gwamnnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce zai mayar da ginin shatale-talen ƙofar gidan gwamnati da ya rusa, zuwa Na’ibawa dake gefen garin Kano. Kakakin gwamnan, Hisham Habib ya sanar da cewa gwamnan da kansa ya kai matar da ta zana ginin, Kaltume Gana zuwa in da za a sake sabon ginin. Gwamnan ya ce  wurin […]

Gwamnan Kano zai mayar da ginin shataletalen da ya rusa

Kaltume Bulama Gana da kek din da Kungiyar masu gashin burodi ta gasa na shatale-talen da ta zana don karramawa

Gwamnnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce zai mayar da ginin shatale-talen ƙofar gidan gwamnati da ya rusa, zuwa Na’ibawa dake gefen garin Kano.

Kakakin gwamnan, Hisham Habib ya sanar da cewa gwamnan da kansa ya kai matar da ta zana ginin, Kaltume Gana zuwa in da za a sake sabon ginin.

Gwamnan ya ce  wurin ya dace da ginin kasancewar ya na bayan gari kuma ba zai haifar da irin ƙalubalen da ya haifar a baya ba.

Za a tada ganuwar Kano da ɓuraguzan rusau

Matar da ta zana shatale-talen da Gwamnatin Kano ta rusa ta magantu

A baya dai, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce  ɗora ginin a shatale-talen gidan gwamnati ya haddasa cunkoson ababen hawa, tare da barazana ga tsaro.

A na ta ɓangaren, mai zanen, Kaltume Gana ta  godewa gwamnan bisa alkinta wanda aka yi shi domin tunawa da cikar jihar Kano shekaru 50 da kafuwa.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu