Gwamnan Katsina na cikin tawagar da suka raka Tinubu ziyarar aiki Birtaniya

Ziyarar dai za ta ɗauki tsawon kwanaki biyu ne, wanda ake sa ran Tinubu zai samu tarba mai kyau.

Gwamnan Katsina na cikin tawagar da suka raka Tinubu ziyarar aiki Birtaniya

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, na cikin tawagar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa Birtaniya.

Ziyarar aikin za ta kasance daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Maris, 2026.

Babban Sakataren Yaɗa Labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya ce halartar gwamnan na nuna muhimmancin hulɗa da ƙasashen waje da kuma ƙoƙarin ƙarfafa dangantaka da su.

Sauran ’yan tawagar sun haɗa da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, Shugaban Majalisar Dattawa, Ministan Shari’a kuma Antoni Janar, Ministan Kuɗi, da Ministan Fasaha da Al’adu.

Haka kuma akwai gwamnonin jihohin Akwa Ibom, Enugu, Ogun, Legas, Zamfara da Filato, tare da wasu manyan jami’an gwamnati da shugabannin ’yan kasuwa.

Ana sa ran Shugaba Tinubu zai samu tarba daga Sarkin Birtaniya, Charles na III, a fadar Windsor.