Gwamnan Katsina ya ceto wanda ’yan ta’adda suka sace

Gwamnan Katsina, Dikko Raddah, ya jagoranci jami’an tsaro wajen fatattar ’yan bidiga a Karamar Hukumar Safana

Gwamnan Katsina ya ceto wanda ’yan ta’adda suka sace

Gwamnan Katsina, Dikko Raddah, ya jagoranci fatattar ’yan bidiga a kauyen Zakka a Karamar Hukumar Safana ta jihar.

Gwamnan ya jagornaci jami’an tsaro hadin gwiwa wajen ceto wani matashi da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi.

Dikko Radda ya jagoranci kai daukin ne a lokacin da ya je karamar hukumar kaddamar da shirin tallafi na mataimakin shugaban majalisar jihar,  Abduljalal Runka.

Sakataren yada labaran gwamna, Kaula Mohammed, ya ce kafin kaddamar da tallafin  ne jami’an tsaro suka samu kiran gagawa cewa ’yan ta’adda sun kai hari kauyen Zakka.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Kaula na cewa, nan take gwamnan ya dakatar da shirin, shige gaba aka fattaki ’yan bindigar, aka ceto matashin.

Daga nan gwamnan ya ba da umarnin kai mutumin asibiti domin kula da shi, saboda harbin sa da aka yi a kafa.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna