Gwamnan Katsina ya raba wa daliban Jihar miliyan 640 a matsayin tallafin karatu
Kowanne daga cikin daliban ya samu 50,000
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya raba wa wasu hazikan daliban Jihar su 210 tallafin karatu na Naira 50,000 kowanensu domin kara masu kwarin gwiwa.
Daliban dai sun fito ne daga manyan makarantun Jihar kuma Gwamnan ne ya ba su daga aljihunsa.
- An ci tarar Kano Pillars miliyan daya kan kutsen magoya baya cikin filin wasa
- An yanke wa likitan da ya yi wa ’yar uwar matarsa fyade daurin rai da rai
An dai gudanar da bikin raba tallafin ne a harabar Hukumar Bayar da Tallafin Karo Karatu ta Jihar a ranar Litinin, kuma an bayar da shi ne ga dalibai masu maki (CGPA) 4.50 zuwa sama.
A jawabinsa yayin kaddamarwar, Gwamna Dikko ya ce shirin na nuna yadda gwamnatinsa ta damu matuka da kokarin samar wa daliban da ke karatu a manyan makarantu sauki a karatunsu.
Ya ce, “Za mu ci gaba da saukaka wa hazikan dalibanmu hanyoyin karatunsu. Mun biya wannan tallafin ne domin rage wa dalibai da iyayensu radadin da suke ciki.
“Wannan kuma wani shiri ne da nake da shi na inganta rayuwar wadannan daliban domin su fuskanci karatunsu yadda ya kamara. Hakan zai kara sa daliban su jajirce,” in ji Gwamna Radda.
Kowane dalibi an bashi wannan tallafin na Naira 50,000 daga dukkan wadanda suka bayar da tallafin na kashin kansu.
Gwamnatin Jihar dai ta ware kudin ne domin rabawa daliban da ke karatu a zangon karatu na shekarar 2020/2021 da kuma na shekarar 2021/2022 kamar yadda Babban Sakataren hukumar bayar da tallafin karatu na Jihar, Dokta Aminu Salisu Tsauri ya shaida a jawabinsa a wajen taron kaddamawar.
Daga cikin daliban da suka rabauta da tallafin dai, mutum 14,443 sabbin dalibai ne, yayin da wadanda ke ci gaba da karatun suka kai su 33,492, in ji Babban Sakataren.