Gwamnan Katsina ya sallami duk masu mukaman siyasa

Sabon Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sallami duk masu rike da mukaman siyasa a fadin jihar.

Gwamnan Katsina ya sallami duk masu mukaman siyasa

Sabon Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sallami duk masu rike da mukaman siyasa a fadin jihar.

Sai da ya bar masu mukaman siyasa a Hukumar Jin Daɗin Alhazzan jihar, a matsayin kwamiti, don ci gaba da gudanar da shirye-shiryen aikin Hajjin wannan shekara.

Sabon Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Dangiwa ne ya sanar da haka.