Gwamnan Katsina ya ziyarci matar Janar Rabe a asibiti
Radda ya yaba da jarumtaka da kwarewar sojojin, yana mai cewa nasarar ta nuna jajircewar rundunar wajen kare rayuka da tabbatar da tsaro a Katsina da yankin Arewa maso Yamma.
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ziyarci Hajiya Amina Rabe Abubakar, matar marigayi Janar Rabe Abubakar, a Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da ke Katsina, bayan da sojojin suka kubutar da ita daga hannun ’yan bindiga.
A ranar Talata Gwamnan ya ziyarce ta ne tare da Darakta Janar na Hukumar Yaɗa Labarai ta Jihar Katsina, Maiwada Dammallam, domin duba lafiyarta da kuma nuna goyon bayan gwamnati.
An ceto Hajiya Amina ne a wani farmaki da sojojin Operation FANSAN YANMAN suka gudanar, inda suka yi artabu da ’yan bindiga har suka samu nasarar kubutar da ita daga hannun masu garkuwa da ita.
Radda ya yaba da jarumtaka da kwarewar sojojin, yana mai cewa nasarar ta nuna jajircewar rundunar wajen kare rayuka da tabbatar da tsaro a Katsina da yankin Arewa maso Yamma.
- Gwamnatin Katsina ta haramta sana’ar POS da cajin waya
- Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi
- NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana
“Sojojin Operation FANSAN YANMAN sun nuna jarumtaka da kwarewa wajen aikin da suka yi. Wannan nasara ta kara tabbatar wa al’ummar Katsina cewa yaki da ’yan bindiga yana gudana da sabuwar himma,” in ji gwamnan.
Ya ce nasarar ta nuna yadda ake samun hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da gwamnati wajen yaki da garkuwa da mutane da sauran laifuka. Radda ya gode wa rundunar sojoji bisa sadaukarwa, tare da tabbatar da goyon bayan gwamnatinsa ga dukkan hukumomin tsaro.
Gwamnan ya yi addu’ar samun sauƙi ga Hajiya Amina, tare da mika ta’aziyya ga iyalan marigayi Janar Rabe Abubakar.