Gwamnan Kebbi ya nanata kudirinsa na samar da ribar dimokuradiyya ga jama’a
Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya kara nanata kudirinsa na samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar.Gwamna Bagudu ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a kan cikarsa shekara daya a kan kujerar Gwamna a masaukin Shugaban kasa da ke Birnin Kebbi.Gwamna Atiku Bagudu ya ce, duk da […]
Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya kara nanata kudirinsa na samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar.
Gwamna Bagudu ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a kan cikarsa shekara daya a kan kujerar Gwamna a masaukin Shugaban kasa da ke Birnin Kebbi.
Gwamna Atiku Bagudu ya ce, duk da matsalar tattalin arziki da ake fama da ita, gwamnatin jihar ta gudanar da wasu muhimman ayyuka a fannin samar da wutar lantarki a babban birnin jihar da wasu kananan hukumomi inda ake daukar awa 24 ba a dauke wutar lantarki ba, sai da kwakkwaran dalili. Ya ce a fannin ilimi, sun fara sayo kayayyankin aiki kamar tebura da kujeru da littattafai da kuma tantance malaman kwarai da kuma ba dalibai abinci mai inganci.
Da Gwamnan ya koma bangaren noma, ya ce jihar ce kan gaba a jihohin Arewa wajen noman shinkafa rani da damina, inda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da noman shinkafa ta rani da kuma ba manoman jihar tallafin yin noma da aka kashe biliyoyin Naira don tallafa wa manoman shinkafa da alkama.
Gwamna Bagudu ya ce yanzu haka gwamnatinsa ta sayo takin zamani na Naira miliyan 700 don raba wa manoman damina a kan farashi mai sauki.
Gwamna Abubakar Bagudu ya ce duk ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a cikin shekara daya da ta gabata musamman giggina sababbin hanyoyi a garuruwan Birnin Kebbi da Yawuri da kuma inganta asibitoci da makarantu da wutar lantarki, ta yi su ne da nufin kafa kwakkwaran harsashin ci gaban jihar.
Ya ce idan aka ci gaba da ayyuka a jihar kamar yadda aka yi ashekarar da ta gabata, nan da shekara bakwai masu zuwa duk makarantu da asibitoci da hanyoyin jihar za su kasance ingantattu a yayin da kowane gari zai samu abubuwan more rayuwa.