Gwamnan Kogi: Kotun Koli ta yi watsi da jam’iyyar DPP
Kotun Koli ta ci jam’aiyyar da dantakarta tara saboda karancin shekarunsa
Kotun kolin Najeriya
Kotun Koli ta yi watsi da daukaka karar da dan takara jam’iyyar DPP a zaben Gwamnan Jihar Kogi, Usman Imam Mohammed ya yi zuwa gabanta.
Kotun ta umarci jam’iyyar da dan takarar nata su biya Gwaman Jihar Yahaya Bello tarar Naira 400,000 sannan su ba mataimakin sa Edward Onoja N200,000.
Alkalan Kotun Kolin karskashin Mai Shari’a Tanko Muhammad sun yi kakkausan suka ga lauyan DPP M.S Ibrahim da ya daukaka karar wanda suka ce ya saba doka saboda karancin shekarun mai shigar da karar.
DPP da dan takarar nata na kalubalantar cire su daga zaben Gwamnan Jihar Kogi da aka gudanar a watan Nuwamban 2019.
Amma da alkalan suka tambayi shekarun wanda yake karewa, lauyan M. S Ibrahim ya shaida musu cewa shekarunsa 31, sabanin shekara 35 da doka ta shardanta wa masu takarar kujerar gwamna.
Ya ce, “Na amince cewa daukaka karar ba ta da fa’ida, don haka ina neman izinin janye ta”, inji lauyan.
Akalan sun yi masa kashedi cewa, “ba bata lokaci muka zo yi ba. Wannan daukaka kara abu ne na ilimi”.
– Kotun Koli ta dage sauraron ‘yan takara PDP da SPD
Gabanin haka alkalan sun sanya ranar 21 ga Agusta, 2020 domin yanke hukunci a kan daukaka kara kan zaben da dan takarar jam’iyyar PDP, Inuwa Wada ya yi.
Wada na kalubalantar nasarar Gwamna Yahaya Bello a zaban saboda kurakuran da ya ce aka tafka.
A ranar ne kuma kotun za ta saurari karar da ‘yar takarar jam’iyyar SPD, Natasha Akpoti ta daukaka kan makamancin zargin.