Gwamnan Kogi ya kori Kwamishina da wasu 2 daga aiki

An sanar da sallamarsu daga aiki cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan ta fitar.

Gwamnan Kogi ya kori Kwamishina da wasu 2 daga aiki

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya kori kwamishinan noma, Mista David Apeh daga aiki.

Har wa yau, gwamnan ya kori mataimakinsa na musamman kan harkokin agajin gaggawa, Mista Danladi Isah-Yunusa, da Hajiya Maryam Salifu, shugabar hukumar kula da yawon bude ido ta jihar.

Korar tasu na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar, Misis Folashade Ayoade-Arike, ta fitar a Lokoja.

Ko da yake ba a bayyana dalilin da ya sa gwamnan ya sallame su daga aiki ba.

Sai dai ta ce an sallami Isah-Yunusa da Salifu daga aikinsu ne saboda rashin da’a.

Baffa Bichi da Barau Jibrin sun gana a Abuja

MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP

Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas

Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo