Daga LegasKiwon LafiyaLabaraiUncategorized• Created May 2, 2020 13:02
HOTUNA: Sabuwar cibiyar killace masu coronavirus a Legas
A ranar Juma’a 1 ga watan Mayu gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar da wata sabuwar cibiyar killace masu dauke da cutar coronavirus mai gado 118, a yankin Gbagada. Mista Sanwo-Olu ya kaddamar da cibiyar ne a daidai lokacin da jihar ke fuskantar karancin wuraren jinyar masu dauke da cutar, lamarin da ya sanya […]
A ranar Juma’a 1 ga watan Mayu gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar da wata sabuwar cibiyar killace masu dauke da cutar coronavirus mai gado 118, a yankin Gbagada.
Mista Sanwo-Olu ya kaddamar da cibiyar ne a daidai lokacin da jihar ke fuskantar karancin wuraren jinyar masu dauke da cutar, lamarin da ya sanya mahukunta fara tunanin yiwuwar killace majinyatan a gidajensu.
Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu tare da kwamishinan lafiya na jihar Akin Abayomi da wasu ma’aikatan cibiyar killace majinyata ta Bgagada a Legas
Wani bangare na cibiyar
Wasu daga cikin gadajen majinyata 118 na cibiyar killace majinyata ta Gbagada, a Legas
Wani sashe na cibiyar killace masu dauke da Coronaviru ta Gbagada
Kofar shiga cibiyar killace masu coronavirus ta Gbagada mai gadajen asibiti 118 wadda gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar
Hoton ginin cibiyar daga sama
Sashen tarbar baki na cibiyar
Gadajen majinyata na cibiyar killace masu Coronavirus