Gwamnan Nasarawa ya kori Sakataren Gwamnatin jihar da wasu
Rahotanni na bayyana cewa, wasu na ganin rushe hadiman Gwamnan zai yi tasiri sosai wajen gudanar da harkokin mulki da aiwatar da manufofin jihar.
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya rusa Majalisar Zartarwar Jihar tare da korar Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Muhammad Aliyu-Ubamdoma da kuma dukkanin hadimansa na musamman.
Aminiya ta samu rahoton cewa Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa na musamman da aka gudanar a gidan gwamnati da ke garin Lafia babban birnin jihar a ranar Juma’a.
- Mutum ɗaya ya mutu a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa
- Ɗan Sanda cikin maye ya saki masu laifi 13 don murnar sabuwar shekara
Jim kaɗan bayan tafiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shetima wanda ya kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya a jihar domin ƙaddamar da wasu ayyuka a cikin jihar.
Wakilinmu ya kuma ruwaito cewa, ana sa ran rushe hadiman Gwamnan zai yi tasiri sosai wajen gudanar da harkokin mulki da aiwatar da manufofin jihar.
Sai dai wani babban jami’in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, duk da cewa har yanzu ba a bayyana dalilan da suka haddasa korar ma’aikatan gwamnatin ba, amma ya ce Gwamna Sule ya yi fice wajen yin garambawul ga tsarin tafiyar da harkokin gwamnatin jihar.
Wakilinmu ya kuma ruwaito cewa, a shekarar 2021 Gwamnan Sule ya rusa Majalisar Zartaswar Jihar, saboda buƙatar samar da tsarin gudanar da mulki mai inganci.