Gwamnan Neja bai yi adalci ba – Hukumar Aikin Hajji

Gwamnan ya zargi NAHCON da gaza gudanar da aikin Hajjin bana yadda ya kamata.

Gwamnan Neja bai yi adalci ba – Hukumar Aikin Hajji

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta bayyana rashin jin dadinta kan zargin da gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi mata na rashin shirya ingantaccen aikin Hajji a bana.

NAHCON ta ce gwamnan bai yi mata adalci ba idan aka yi la’akari da yadda darajar Naira ta faɗi warwas.

Bago, ya yi zarge-zargen a wani taron manema labarai a ƙasar Saudiyya, inda ya buƙaci a dawo da ɗawainiyar alhazai ƙarƙashin jagorancin jihohi.

Mai magana da yawun NAHCON, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta ce ƙasar Saudiyya ba ta hulɗa da jihohi a kan harkar aikin Hajji.

“Ba zai yiwu a ce Jihar Neja ta je Saudiyya don yin yarjejeniya kan alhazanta ba. Idan gwamnan ya ce a ɗauki ayyukan a mayar da su kan jihohi akwai ayar tambaya a kai,” in ji ta

Gwamnan na Neja ya yi zargin cewa NAHCON ta gaza samar wa alhazai yanayin da za a kula da lafiyarsu, duba da makudan kuɗaɗe da suka biya domin yin aikin Hajji.

“Muna sonmu tunatar da gwamna Bago cewa hukumomin jihohi ne ke zaɓar waɗanda za su ciyar da alhazansu da kuma irin abincin da suke so ba wai hukumar mu ba.”

Ta kuma yi watsi da batun cewa NAHCON ta gaza a ayyukanta na gudanar da aikin Hajji.

Idan ba a manta a ranar Lahadi ne gwamnan ya yi wa NAHCON kaca-kaca kan tallafin kuɗin aikin Hajji da gwamnatin tarayya ta ba ta a bana.

Ya buƙaci ƙungiyar gwamnoni da ta mara masa baya kan neman a bai wa jihohi damar gudanar da aikin Hajji a nan gaba.

Mutanen gari sun kashe ɗan bindiga a Kaduna

Jabun Kayayyaki: NAFDAC ta rufe shaguna 100 a Enugu

Ya shiga hannu kan damfarar mahajjata Naira miliyan 4.5

Bankin Duniya ya ba Nijar tallafin biliyan 214