Gwamnan Ondo Akeredolu ya rasu

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya rasu yana da shekaru 67 bayan fama da jinya,

Gwamnan Ondo Akeredolu ya rasu

Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na Jihar Ondo ya rasu a safiyar Laraba bayan fama da rashin lafiya.

Gwamna Akeredolu, babban lauya (SAN) ne kuma tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), ya rasu yana da shekaru 67 bayan fama cutar kansar jini, Leukemia.

Iyalai da jami’an gwamnati sun tabbatar cewa gwamnan, wanda ke wa’adinsa na biyu ya rasu ne a daidai lokacin da ake kokarin fitar da shi kasar waje.

A watan Satumba ne Akeredolu ya dawo Najeriya bayan jinyar watanni uku a kasar Jamus.

A baya-bayan nan ne kuma yake shirin komawa kasar waje domin jinya bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarce shi da ya mika ragamar jihar ga mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa.

Alokacin da ya tafi kasar Jamus Lucky Aiyedatiwa ne yake gudanar da mulkin jihar matsayin mukaddashin gwamna.

Tun bayan dawowar Akeredolu a watan Satumba, yake zaune a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, inda yake gudanar da harkokin mulki daga nan, lamarin da ya kawo ce-ce-ku-ce,har wasu na neman ya sauka daga kujerarsa.

Ranar 9 ga watan yuli, mai dakin Akeredolu, Betty ta soke bikin da aka shirya na zagayowar ranar haihuwarsa.

An soke bikin ne a daidai lokacin da wasu ke surutai cewa ana shirin shagali alhali gwamnan ba shi da cikakkiyar lafiya.

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7