Gwamnan Ondo ya dawo gida bayan sama da wata 3 yana jinya a Jamus

Tuni mukarraban Gwamnan suka je Ibadan domin su tarbe shi

Gwamnan Ondo ya dawo gida bayan sama da wata 3 yana jinya a Jamus

Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya dawo Jihar bayan shafe kimanin wata uku yana jinya a kasar Jamus.

Bayanai sun nuna tuni mukarraban gwamnatin suka isa Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, domin su tarbe shi.

Tun a watan Yuni ne dai Gwamnan ya tafi hutun neman lafiya na wata daya, kafin daga bisani ya nemi Majalisar Dokokin Jihar da ta tsawaita masa shi.

A lokacin dai ya mika ragamar mulkin Jihar a hannun mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya bukata.

Hotuna da bidiyon Gwamnan dai a wani asibiti a kasar Jamus lokacin da yake bikin cika shekara 67 da haihuwa.

A cikin bidiyon, an ga Gwamnan yana tikar rawa tare da matarsa da kuma wasu abokansa.

Wata majiya ta ce Gwamnan zai isa Ibadan inda zai huta na ’yan kwanaki kafin ya wuce Jihar ta Ondo.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan