Gwamnan Ondo ya sa tsare mutumin da ya ayyana kansa a matsayin sarki
Gwamnatin ta ce har yanzu babu wanda nada kowa a matsayin Olofun na Masarautar Irele
Gwamna Rotimi Akeredelu na Jihar Ondo ya bayar da umarnin gaggawa ga Kwamishinan ’Yan Sandan jihar ya hanzarta kamo wani mutumi mai suna Ademola Idowu Oloworiyibi da yake kiran kansa a matsayin Olofun na Masarautar Irele.
Bayanin haka yana kunshe ne cikin wata wasika da gwamnan ya aika wa kwamishinan ’yan sandan a ranar Alhamis.
- Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da ya fi kowa yawan zuri’ar mahaddata Alkur’ani a duniya
- Ma’aikaciyar Google ta ajiye aiki saboda nuna wa Falasdinawa bambanci
Wasikar mai dauke da sanya hannun Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar, Cif Olugbenga Ale, ta kara da cewa matakin da Ademola Idowu Oloworiyibi ya dauka na kiran kansa a matsayin Olofun na Masarautar Irele haramtacce ne kuma zai iya tayar da zaune tsaye a tsakanin al’ummar masarautar da suke zaune lafiya.
Gwamnatin ta ce har zuwa lokacin aikawa da wasikar, ba a tabbatar da nada kowa a matsayin Olofun na Masarautar Irele ba.
Saboda haka aka umarci kwamishinan ’yan sandan ya hanzarta cika aiki wajen kama mutumin domin hukunta shi.