Gwamnan Ondo ya sallami kwamishinoni da masu ba shi shawara
Gwamnan ya umarci kwamishinonin da su dawo da duk kayan gwamnaitin da ke hannunsu
Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya sallami daukacin kwamishinoni da hadimai da masu ba shi shawara nan take.
Gwamnan ya kuma umarci kwamishinonin da su mika duk kayan gwamnaitin da ke hannunsu ga Manyan Sakatarorin ma’iakatun ko kuma jami’ai mafiya girman mukami.
“Gwamnan yana umartar wadanda wannan mataki ya shafawa da su dawo da duk kayan gwamnati da ke hannunsu,” in ji sanarwar rushe majalisar kwamishinonin da sallamar hadiman da sakataren yada labaran gwamnan, Prince Ebenezer Adeniyan, ya fitar.
Sanarwar ta kara da nuna godiyar Gwamna Aiyedatiwa a gare su, kan hidimar da suka yi wa jihar.
- An ci gaba da kashe-kashe duk da dokar hana fita ta sa’a 24 a Filato
- Ya mutu bayan lalata da matar aure a otel
Wannan mataki na zuwa ne makonni uku da zaman Aiyedatiwa gwamnan a sakamakon rasuwar mutuwar fuju’ar Gwamnan Rotimi Akeredolu wa watan Disamba.
Kafin rasuwar Akeredolu dai dangantaka ta yi tsami tsakansin su, har ta kai ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya baki, amma duk da haka, haka ba ta cim- ma ruwa ba.