Gwamnan Osun ya dakatar da ayyukan NURTW sakamakon rikici a tashoshin mota
Gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su karɓe ragamar ayyukan tashoshin mota a jihar.
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya dakatar da dukkanin ayyukan ƙungiyar masu motocin sufuri (NURTW) a tashoshin motocin haya na faɗin jihar.
An ɗauki wannan mataki ne bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu na ƙungiyar a ranar Litinin a Osogbo, babban birnin jihar.
- Manyan ‘yan bindigar da aka halaka a Arewa maso Yamma
- An gano gawar ɗalibin Jami’ar Kashere bayan ɓacewarsa
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Kolapo Alimi, ya fitar a madadin gwamnan, an bayyana cewa umarnin ya fara aiki nan take.
Sai dai gwamnatin ta ce ba za a rufe tashoshin motocin ba.
Gwamnan ya ce an yanke wannan hukunci ne a taron Majalisar Tsaron Jihar domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a dukkanin tashoshin motocin haya.
Ya kuma umarci rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro su tabbatar da dakatar da dukkanin ayyukan NURTW a tashoshin motocin jihar.
Haka kuma, gwamnan ya hana ƙungiyar karɓar duk wani kuɗi a tashoshin motocin, tare da umartar jami’an tsaro su kama duk wanda ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin jami’in NURTW.