Gwamnan Oyo ya lashe amansa kan daga darajar Hakimai 21 zuwa ‘Sarakuna’
Daga cikin su har da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rasheed Ladoja
Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya sake dawo da martabar Hakimai 21 da tun farko gwamnatinsa ta dakatar da su daga kiran kansu a matsayin Sarakuna a masarautar Ibadan.
Daga cikin su har da tsohon Gwamnan Jihar Sanata Rasheed Ladoja.
- Bin diddigi: Shin da gaske an bude bodar Legas don shigo da motoci?
- Legas ne birni na hudu mafi rashin dadin zama a duniya – Rahoto
Marigayi tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Abiola Ajimobi ne ya daukaka darajar manyan masu rike da sarautu da hakimai 21 zuwa Sarakuna wato (Oba) masu sandar girma a masarautar ta Ibadan.
Amma a lokacin da ya kama ragamar mulki a shekarar 2019, Gwamna Makinde ya tube rawunan da tsohuwar Gwamnati ta nada wa wadannan manyan mutanen su 21 da aka mayar da su matsayinsu na farko.
Bayanin da Aminiya ta samo da sanyin safiyar Alhamis ya nuna cewa wata majiya mai tushe daga ofishin Gwamna ta ce a ranar 7 ga watan Yuli mai zuwa ne Mai Martaba Olubadan na Ibadan, Oba Lekan Balogun zai sake sanya wa wadannan manyan masu sarauta 11 hular sarauta da mika masu sandar girma domin tabbatar da su a matsayin Sarakuna wato (Oba) a masarautar Ibadan.
Hakan ya biyo bayan sanya hannu a kan dokar sarautu da Majalisar Dokokin Jihar ta yi wa gyara ta zama doka ne da Gwamnan ya yi kwanan baya.
Sake daukaka darajar sarakunan da Gwamnati ta yi ya biyo bayan shawarar da Olubadan na Ibadan, Oba Lekan Balogun ya bayar ne, in ji majiyar.
Manyan masu sarauta 11 da Gwamnati ta sake daukaka darajar su zuwa Sarakuna sun hada da Balogun na Ibadan Cif Owolabi Olakulehin da Otun na Ibadan Cif Rasheed Ladoja da Otun Balogun Cif Tajudeen Ajibola da Osi Olubadan Cif Eddy Oywole da Osi Balogun Cif Lateef Adebimpe.
Sauran sun hada da Ashipa Olubadan Cif Biodun Kola-Daisi da Ashipa Balogun Cif Kola Adegbola da Ekerin Olubadan Cif Hamidu Ajibade da Ekerin Balogun Cif Olubunmi Isioye da Ekarun Olubadan Cif Bayo Akande da Ekarun Balogun Cif Abiodun Azeez.
Da take kare matakin tube hular sarautar da sake tabbatar da nadin da Gwamnan ya yi, majiyar ta ce marigayi tsohon Gwamna Abiola Ajimobi ya yi babban kuskure a wancan lokaci wajen yanke shawarar nada wadannan mutane har da wadanda basu cancanta ba.