Gwamnan Oyo ya musanta zargin shirin karfa-karfa a zaben 2019
Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya yi wani taron ganawa da magoya bayan Jam’iyyar APC a mazabarsa ta Oyo ta Kudu inda ake cewa zai tsaya takarar Sanata a mazabar a zabe mai zuwa bayan ya kammala wa’adinsa na Gwamna. Sai dai cikin jawabinsa bai yi wata magana da ta shafi haka ba amma […]

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya yi wani taron ganawa da magoya bayan Jam’iyyar APC a mazabarsa ta Oyo ta Kudu inda ake cewa zai tsaya takarar Sanata a mazabar a zabe mai zuwa bayan ya kammala wa’adinsa na Gwamna. Sai dai cikin jawabinsa bai yi wata magana da ta shafi haka ba amma ya tabbatar wa magoya bayan cewa Jam’iyyar APC ba za ta tilasta dora ’yan takarar mukamai a zaben na badi ba.
Haka Gwamnan ya kare kansa game da zargin cewa yana nuna fiffiko da goyon bayan wadansu masu sha’awar tsayawa takarar kujerar Gwamna fiye da wadansu a cikin Jam’iyyar APC. Ya ce “Ba haka al’amarin yake ba amma na san cewa ina karfafa wa dukansu gwiwa su fito a fafata da su domin dukansu mutanena ne. Ni kadai ba zan taba tilasta dora dan takara ba amma za mu hadu da sauran jama’a mu goyi bayan kowane dan takara da ya fi kowa cancanta.”
Gwamna Ajimobi ya tabo matsalar jam’iyyar ta APC a Jihar Oyo, inda ya ce “Wadansu miyagun mutane ne suka haddasa rikicin da muka fuskanta a cikin jam’iyarmu kwanan baya a Jihar Oyo. Su ne suke daukar nauyin ingiza wannan bangare na (Unity Group) da suka kaurace daga cikinmu. Amma abin farin ciki shi ne ballewar da suka yi bai rage mana komai ta fannin yawan magoya baya ba domin har yanzu mu ne a kan gaba.”
Ya shaida wa magoya bayan cewa, taron da suka yi da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja a makon jiya an gudanar da shi ne domin tattaunawa a kan samo hanyar daukaka matsayi da darajar Jam’iyyar APC, ta yadda za ta yi nasarar lashe zaben badi da ke gabatowa.
Wani bincike da Aminiya ta gudanar, ya nuna cewa idan Gwamna Abiola Ajimobi ya nemi tsayawa takarar Sanata a zabe mai zuwa to akwai yiwuwar sake samun baraka a Jam’iyyar APC a jihar. Masu fadin haka sun dogaro ne da kasancewar Sanata Soji Akanbi da ke kan kujerar a zango na farko a mazabar Oyo ta Kudu wanda shi ma ke son yin ta-zarce a zango na biyu.
Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Oyo da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “A gaskiya kamata ya yi Gwamna Abiola Ajimobi ya koma gefe daya ya shiga cikin sahun dattijan jam’iyya amma muddin ya ce zai nemi wannan kujera to akwai matsala domin shi ma Sanata Soji Akanbi da yake rike da kujerar a yanzu yana so ya sake tsayawa takara a zabe mai zuwa.”