Gwamnan Oyo ya rufe gonar Obasanjo kan rashin biyan haraji
Gwamnatin Jihar Oyo ta rufe kamfanin gona na tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da wasu kamfanoni 12 saboda kin biyan kudin haraji da ba su yi ba. Hukumar Haraji ta Jihar ce ta dauki matakin rufe kamfanoni da gonakin da suka hada da Kamfanonin MRS Oil da Black Horse da Heinemann Educational Books da Lister […]
Gwamnatin Jihar Oyo ta rufe kamfanin gona na tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da wasu kamfanoni 12 saboda kin biyan kudin haraji da ba su yi ba.
Hukumar Haraji ta Jihar ce ta dauki matakin rufe kamfanoni da gonakin da suka hada da Kamfanonin MRS Oil da Black Horse da Heinemann Educational Books da Lister Flour Mills da Unibersity Press Limited da Ebans Brother da kuma Brooking House. Sauran kamfanonin su ne Group Medical Hospital da Butterfield Bakery da Chicken Republic da kuma Rasmed Publicity.
Shugaban Hukumar Tarttara Haraji ta Jihar, Mista Bicci Alli, ya bayyana cewa daukar matakin ya zama dole ganin cewa gwamnati ta dade tana yi wa wadannan kamfanoni tuni domin su biya harajin nasu amma suka yi biris da batun.
Haka kuma wannan aiki da hukumar ta yi ya shafi wasu bankuna da suka hada da Diamond da Stanbic IBTC da Skye da FCMB da Heritage da Unity da Ecobank da UBA da Keystone da First Bank da kuma Union Bank.
“Wannan abu kuma ba rana guda ba ne. Mun dade muna ta yi wa wadannan kamfanoni tuni kan kudaden haraji amma suka yi kunnan kashi kamar ba da su ake yi ba. Sannan babu wata doka da muka saba game da daukar wannan mataki,” inji Mista Alli.