Gwamnan Oyo ya rusa Rundunar YES-O

Gwamnan Jihar Oyo Alhaji Abiola Ajimobi ya rusa Rundunar Inganta Rayuwar Matasa ta Jihar Oyo (Youth Empowerment Scheme of Oyo State, YES-O). Rundunar mai dauke da matasa maza da mata dubu 20, an kafa ta ce a ranar 1 Disambar shekarar 2001 domin tsara yanayi da tsabtace gari da tabbatar da jama’a sun yi aiki […]

Gwamnan Oyo ya rusa Rundunar YES-O
Gwamnan Oyo ya rusa Rundunar YES-O

Gwamnan Jihar Oyo Alhaji Abiola Ajimobi ya rusa Rundunar Inganta Rayuwar Matasa ta Jihar Oyo (Youth Empowerment Scheme of Oyo State, YES-O).
Rundunar mai dauke da matasa maza da mata dubu 20, an kafa ta ce a ranar 1 Disambar shekarar 2001 domin tsara yanayi da tsabtace gari da tabbatar da jama’a sun yi aiki da shirye-shiryen gwamnati kamar yadda dokoki suka shimfida.
Gwamnan ya rusa rundunar ce saboda yawan koke-koke da kararrakin da yake samu kan takurawa da karbar kudi ba gaira ba dalili daga jama’a da kwace musu kayayyaki da dakarun rundunar ke yi a sassan jihar.
 Wata takardar sanarwa dauke da sanya hannun Shugaban Rundunar YES-O, Mista Gbenga Olayemi, ya nemi dakarun rundunar su hanzarta mika takardun neman sake daukarsu aiki domin a yi tankade da rairaya da za a kawar da baragurbi daga cikinsu.
 Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa, hukumar gudanarwar Rundunar YES-O, ta aika da dakarunta zuwa ma’aikatu da hukumomi daban-daban domin taimaka musu wajen gudanar da ayyukan da suke neman tsawatarwa da kama masu taurin kai.
Dakarun rundunar sun fi yawa a cikin hukumar tsaftace muhalli da hukumar lura da hanyoyi (OYRTMA) da ta tantance takardu da ingancin abubuwan hawa (BOTAbED).
Dokar hana talla a gefen hanya da na tsabtace muhalli da gwamnatin jihar ta kafa ne wasu dakarun YES-O ke amfani da su wajen musguna wa ’yan kasuwa masu karamin karfi da ta kwace kayansu.
A hukumomin lura da hanyoyi da tantance takardun abubuwan hawa, suna yin tarar Naira dubu 10 zuwa sama ga duk motar da aka sanya jiniya ta kawar da ita daga kan hanya. Su kuwa masu babur suna biyan tarar Naira dubu 3 zuwa sama ne a dalilin samunsu da takardun mallaka na bogi da kasa biyan haraji.
Sai dai kuma, binciken ya nuna cewa, aikin tantance takardun abubuwan hawa da hukumomin biyu suka gudanar a shekara 2 da kafuwarsu sun taimaka a fannin kama satattun abubuwan hawa masu yawa.
Wani dan okada mai suna Ademola Oyeniyi, ya ce, “A gaskiya ayyukansu babu laifi, sai dai akwai kura-kuran da muke yi da gargadi da shawara ya kamata a yi mana ba kama mu ba.
Kafin Gwamna Ajimobi ya rusa rundunar YES-O ya sha ja kunnen jami’an rundunar kan ayyukansu yi, inda ya ce, yana sane da irin takura wa jama’a da kwace musu kaya da yi musu tarar da suke yi.  
Da yawa daga kananan ’yan kasuwa da suka samu labarin rusa rundunar YES-O, sun yi ta murna sai dai sun nuna rashin jin dadi da suka ji rundunar za ta sake bayyana a kan hanyoyi bayan an yi mata tankade da rairaya.