Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati
A yanzu haka yana ganawar sirri da manyan jami’an tsaro da wakilan gwamnatin tarayya da kuma jami’an gwamnatin jihar.

Sabon Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya isa jihar domin ci gaba da aiki.
Ibas ya isa filin jirgin saman Fatakwal da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar ranar Alhamis inda ya samu tarba daga manyan jami’ai da jami’an tsaro.
- ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno
- Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas
Sabon Gwamnan, tare da rakiyar Kwamishinan ’yan sandan jihar, Olugbenga Adepoju da mataimakin babban sufeton ’yan sanda na shiyya ta 16, nan take suka wuce gidan gwamnati da ke Fatakwal.
Tuni dai Ibas ya isa gidan gwamnati inda wasu jami’an gwamnati suka zagaya da shi harabar gidan.
A yanzu haka yana ganawar sirri da manyan jami’an tsaro da wakilan gwamnatin tarayya da kuma jami’an gwamnatin jihar.
A ranar Talatar nan ne dai shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya naɗa Ɓice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin kantoman jihar Riɓers bayan da ya sanar da ƙaƙaba wa jihar dokar ta-baci. Kuma ya rantsar da shi a ranar Laraba.