Gwamnan Ribas ya ba kungiyar U-23 kyautar Dala dubu 60

Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya cika alkawarin da ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) na ba su kyautar Dala dubu 60 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 14 da dubu 460 saboda nasarar da kungiyar ta samu a kan kasar Kongo a ranar Lahadin da ta […]

Gwamnan Ribas ya ba kungiyar U-23 kyautar Dala dubu 60
Gwamnan Ribas ya ba kungiyar U-23 kyautar Dala dubu 60

Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya cika alkawarin da ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) na ba su kyautar Dala dubu 60 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 14 da dubu 460 saboda nasarar da kungiyar ta samu a kan kasar Kongo a ranar Lahadin da ta wuce.
kungiyar dai ta doke Kongo ne da ci 2 da 1 a kokarin hayewa gasar cin kofin matasa na Afirka da zai gudana a Senegal. Sannan nan da mako biyu ne ake sa ran kungiyar za ta bi Kongo gida a wasa zagaye na biyu da hakan zai sa a tantance kasar da za ta haye zuwa gasar matasan a Senegal.
Tun kafin a gudanar da wasan a Ribas ne Gwamnan ya yi alkawarin ba kungiyar U-23 kyautar Dala dubu 30 ga duk kwallon da suka zura a raga ko kuma kyautar Dala dubu 100 inda suka samu nasarar doke Kongo da ci 3-0 amma sai aka tashi 2-1.
Sai dai a ranar Litinin da ta wuce ne Gwamnan ya gabatar masu da cekin Dala dubu 60 a wani bikin karramawar da ya yi wa daukacin ’yan kwallon da masu horar da su, ciki har da kocin kungiyar Samson Siasia inda ya nuna farin cikinsa a kan nasarar da suka samu a kan Kongo.
“Kun nuna min cewa lallai kun kware a harkar kwallo gannin yadda kuka murza kwallo har kuka samu nasara a kan Kongo.  Ko shakka babu muna sa ran nan gaba da yawanku za su haye zuwa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles don yi wa Najeriya wasa idan kuka dore akan haka, kuma ina alfahari da ku”, inji shi.
A nasa jawabin kocin kungiyar U-23 Samson Siasia ya yaba wa Gwamnan a kan karamcin da ya yi musu, kuma ya yi alkawarin za su ba mara da kunya idan suka ziyarci Kongo a wasa zagaye na biyu nan da makwanni biyu masu zuwa. Sai dai kocin bai ji dadin yadda suka bari har Kongo ta zura kwallo daya a raga ba al’amarin da ya sa suke cikin tsaka mai wuya.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja