Gwamnan Rivers ya rattaba hannu kan kasafin kuɗi Naira tiriliyan 1.1

Gwamnan ya rattaba hannu kan ƙudirin dokar ne a ranar Alhamis, bayan da Majalisar Dokokin Jihar ta amince da shi a ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Oko-Jumbo.

Gwamnan Rivers ya rattaba hannu kan kasafin kuɗi Naira tiriliyan 1.1

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin 2025 da ya kai Naira tiriliyan 1.1.

Fubara ya yi hakan a ranar Litinin lokacin da ya gabatar da kasafin kuɗin bana a gaban ‘yan majalisar dokoki su biyar wanda Victor Oko-Jumbo ke jagoranta.

Gwamnan ya rattaba hannu kan ƙudirin dokar ne a ranar Alhamis, bayan da Majalisar Dokokin Jihar ta amince da shi a ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Oko-Jumbo.

Gwamna Fubara ya dage cewa Martins Amaewhule da wasu mambobi 26 da suka sauya sheƙa daga Jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC sun janye matsayinsu na ‘yan majalisa kamar yadda doka ta tanada.

Ya ce: “Ina so in ce wannan na iya zama ga wasu mutane a wani wuri da har yanzu suke ta cakuɗa al’amura. Muna da Majalisa guda ɗaya kuma Majalisar tana ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Victor Oko-Jumbo ne.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota