Gwamnan Sakkwato na shirin tsige Sarkin Musulmi —MURIC

Gwamna Ahmad Aliyu ya mika wa majalisar dokoki kudurin dokar rage karfin ikon Sarkin Musulmi

Gwamnan Sakkwato na shirin tsige Sarkin Musulmi —MURIC

Mai Alfarma Sarkkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III

Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi (MURIC) ta zargi Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu da yunkurin tube Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.

Babban Daraktan MURIC, Farfesa Isiaq Akintola, ya bayyana takaici bisa abin da ya kira shirin gwamnan na fakewa da dalilinsa na tsige wasu sarakunan gargajiya 15 a matsayin hujjar tube Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.

Sarkin Musulmi shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya da kuma Kungiyar Musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI).

A watan Afrilu ne gwamnan ya Aliyu ya tube wasu sarakunan gargajiya 15 kan laifukan da suka danganci rashin tsaro da kuma rikicin filaye a jihar.

Ya ci gaba da cewa, “a kowane lokaci gwamnan na iya far wa kujerar Sarkin Musulmi da dalilin da ya bayar na tube wadancan sarakuna 15 a kwanakin baya.”

Amma ya jaddada cewa Musulmin Najeriya za su tsaya kai da fata su yaki duk wani yunkuri na tsige Sarkin Musulmi.

Abin da Gwamnatin ta ce

Tuni bangaren zartaswa na Jihar Sakkwato ta mika wa majalisar dokokin jihar kudurin yin gyaran fuska ga dokar masarautun jihar domin dacewa da yanayin jihar.

Dokar masarautum jihar ta yanzu ta damka ikon nada hakiman da dagattai a hannun Majalisar Fadar Sarki.

Amma duk da haka a zahiri shawara kawai fadar take ba wa bangaren gwamnatin, inda a karshe gwamnan jihar ke nada masu sarautun.

Amma da yake karin bayani kan sabuwar dokar, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Sakkwato, Nasir Binji, ya bayyana ce za a yi gyare-gyaren ne nomin ganin tsarin aarautar gargajiya ta yi daidai da tsarin shari’a.

Nasir Binji, ya sanar da manema labarai cewa sabuwar dokar da ake shirin yi ta ba wa Majalisar Sarkin Musulmi ikon mika sunayen mutanen na za a ba wa saraut, amma ta ba wa gwamna ikon yin nadin.