Gwamnan Sakkwato ya gwangwaje ma’aikata da goron Sallah
Daga ranar Alhamis ’yan fansho da sauran ma’aikatan jihar Sakkwato za su fara jin ‘alat’ din kudaden goron Sallah daga
Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu Sokoto, ya ba da umarnin da fitar da kudi domin bayar da goron sallah ga dukkan ’yan fansho da ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi domin bikin Sallar Layya.
Goron sallar, gwamna ya raba shi gida biyu, ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi za a ba su dubu 30 kowanensu.
Masu karbar fansho ds ma’aikatan hukumar lafiya matakin farko za su amfana da dubu 20 suma don shagalin sallah.
Wannan kyautar za a fara biya ne daga ranar Alhamis 13 ga watan Yuni 2024.
- An kama shi da kokon kawunan mutane takwas
- NAJERIYA A YAU: ‘Kananan Hukumomi Na Daf Da Zama Mabarata’
- Mafi Ƙarancin Albashi: Muna kan buƙatarmu ta N250,000 — NLC
Gwamnan ya roki Allah Ya sa a yi shagalin sallah lafiya a jiha da kasa baki daya.