Gwamnan Sakkwato ya raba kekunan guragu 500

Gwamnan Sakkwato ya raba wa guragu 500 kekuna a wani bangare na bikin Ranar Nakasassu ta Duniya a jihar.

Gwamnan Sakkwato ya raba kekunan guragu 500

Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu ya ƙaddamar da rabon kekunan guragu 500 a wani bangare na Ranar Nakasassu ta Duniya a jihar.

Gwamnan ya ce manufar hakan ita ce tallafa wa nakasassun tare da tabbatar da cewa sun ci gaba da cin moriyar gwamnati.

“Hakan na cikin tsarinmu na tabbatar da cewa kowanne bangare na al’umma ya amfana da shirye-shiryen gwamnati.

“Domin tabbatar da cewa an samar wa musu da ci-gaba mai ɗorewa a wannan jiha tamu, mun yi tanadi a kasafin kuɗin shekarar 2025 domin gyara makarantar masu bukata ta musamman ta A.A Raji domin bunƙasa iliminsu.

“Mun kuma yanke shawarar ƙara adadin waɗanda ke amfana da alawus din wata-wata da muke ba wa mutane 6,679 zuwa mutane 10,000 tare da fara shirye-shiryen raba kekunan guragu kashi na biyu domin ci gaba da inganta rayuwar masu buƙata ta musamman a Jihar Sakkwato.

“Gwamnati na amfani da wannan dama domin gode wa tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma sanata mai wakiltar Sakkwato ta Arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko bisa tallafin N10,000 da ya ba wa masu buƙata ta musamman guda 6,679 domin wannan rana.

“Za mu ci gaba da jajircewa wajen inganta rayuwar al’umar wannan jiha a kowanne mataki,” a cewar gwamnan.