Gwamnan Sakkwato ya sa hannu kan dokar rage ikon Sarkin Musulmi
Sabuwar dokar masarautun Sakkwato ta kwace wa Sarkin Musulmi damarsa ta nada hakimai da dagatai.
Gamayyar Kungiyoyin Musulmi Najeriya (CMON) ta bukaci gwamnatin Sakkwato ta kara wa Fadar Sarkin Musulmi karfin iko ta yadda duk mai rike da kujerar Sarkin Musulmi ba zai zama abin wasa ko dan amshin shata ga ’yan siyasa ba.
A ranar Alhamis gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, ya sanya hannu kan dokar da ta yi wa masarautun jihar gyaran fuska.
Dokar da ta jima tana tayar da kura, ta haramta wa Sarkin Musulmi damarsa ta nada hakimai da dagatai.
A bisa sabuwar dokar, Sarkin Musulmi zai iya ba da shawarar sunayen wadanda yaje so a nada, amma gwamna ke da wuka da nama.
- An yanke wa ’yan daba 106 hukunci a kwana 10 a Kano
- Kotu ta tura tsohon ministan lantarki zuwa gidan yari
Wannan mataki dai ya haifar da ce-ce-ku-ce tun ba yanzu ba, inda kungiyar Musulmi ta MURIC ta zargi gwamnatin jihar da yunkurin tsige Sarkin Musulmi kamar yadda aka yi wa wasu hakimansa 15.
Amma gwamnatin ta bayyana cewa sabuwar dokar ba da ta niyyar tube Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar,
Kakakin gwamnatin, Sambo Danchadi, ya ce, hasali ma, inganta tsarin masarautun jihar dokar ta yi.
Ta kara da cewa hakan zai ba da damar yanka wa hakimai da dagattai albashi.
Amma shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi zargin dokar na shirin rage karfin ikon Sarkin Musulmi.
A ranar Alhamis wata gamayyar kungiyoyin Musulmi 33 (CMON) ta bukaci gwamnatin jihar ta kara wa Sarkin Musulmi karfin iko ta yadda zai kara kima a matsayin shugaban al’ummar Musulmi a Najeriya.
Kungiyar ta yi kira da a yi dokar da za ta hana tsige sarkin Musulmi a matsayin na shugaban Musulmi a Najeriya.
A jawabinsa, kakakin CMON, Alhaji Abdur-Rahman Balogun, ya roki Shugaba Tinubu da gwamnan Sakkwato da su dakatar da duk wani mataki da ke iya rage darajar kujerar Sarkin Musulmi, uwa uba batun tsige shi.