Gwamnan Taraba ya rage wa daliban jami’a rabin kudin makaranta

Ya ce an yi sassaucin ne saboda rage radadin cire tallafin man fetur

Gwamnan Taraba ya rage wa daliban jami’a rabin kudin makaranta

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya sanar da rage kudin makaranta ga daliban jami’a a Jihar da kaso 50 cikin 100 domin rage musu radadin janye tallafin man fetur.

Kakakin Gwamnan, Emmanuel Bello ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba, inda ya ce ya ba da sanarwar ce a Jami’ar Jihar sannan ya jaddada muhimmancin ilimi a gwamnatinsa.

Gwamnan ya kuma ce tuni ya jima da ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi.

Sanarwar ta ce, “Na damu matuka wajen samar da ilimi kyauta a matakan Firamare da Sakandare na jiharmu.

“Daliban jami’a da dama sun nuna jin dadinsu da wannan matakin, inda suka ce ragin zai bunkasa rayuwarsu sosai.

“Wasu ma daga cikin iyayen daliban wadanda ke cikin tsaka mai wuya sakamakon cire tallafin sun ce dama laluben inda za su samo kudin ya tsaya musu a rai, don haka sun ji dadi sosai.”

A wani labarin kuma, Gwamna Agbu Kefas ya ce sun kammala wasu ingantattun tsare-tsare wajen biyan ’yan fansho da tsofaffin ma’aikata.

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024