Gwamnan Yobe ya nada hadimai 30 kan shafukan zumunta
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya nada mutum 30 a matsayin masu taimaka mishi na musamman kan shafukan sada zumunta. Sakataren Yada Labara na Ofishin Sakatare Gwamnatin Jihar Yobe, Shuaibu Abdullahi, ya sanar da hakan. Da sabbin nade-naden, yanzu yawan hadiman gwamnan ya karu zuwa 672. Kafin nadin da aka yi wa mutum 30 […]
Mai Mala Buni
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya nada mutum 30 a matsayin masu taimaka mishi na musamman kan shafukan sada zumunta.
Sakataren Yada Labara na Ofishin Sakatare Gwamnatin Jihar Yobe, Shuaibu Abdullahi, ya sanar da hakan.
Da sabbin nade-naden, yanzu yawan hadiman gwamnan ya karu zuwa 672.
Kafin nadin da aka yi wa mutum 30 din, Gwamna Buni na da hadimai da masu ba shi shawara guda 643 ciki har da manyan mashawarta da sauran jami’ai.