Gwamnan Yobe ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 20
Gwamnan Yobe ya rantsar ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 20
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a ranar Asabar ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 20 da za su gudanar da kula da ma’aikatun Jihar.
Da ya ke jawabi yayin rantsar da su, Gwamnan ya bukaci sabbin Kwamishinonin da su kara himma da kwazo wajen sauke nauyin da aka dora musu.
- Spain ta lashe kofin duniya na mata a karon farko
- ’Yan bindiga sun sace Kansila da wasu mutum 2 a Kaduna
Gwamnan ya taya su murna da nadin da aka yi musu, a matsayinsu na Kwamishinoni kuma mambobin Majalisar Zartarwar Jihar.
Ya ce, “Na tabbata kuna sane da aikin da ke jiran ku, na daukar matakai masu mahimmanci a madadin jama’armu, wajen aiwatar da manufofinmu da shirye-shiryenmu wajen haɓaka ci gaban Jihar da a kan ta ne muka tabbatar wa al’umma wa’adin mulkin mu karo na biyu, a zaben Gwamna na 2023 bisa alkawuran da muka dauka na shimfida musu ayyukan rays kasa da kula da bukatun su.
“Ina mika godiya ta ga Mai Girma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe da kuma ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Yobe bisa mahimmancin da suka bayar wajen tantance kwamishinonin.”