Gwamnan Zamfara ka biya wa dalibai kudin jarabawa

Kai tsaye nike son Editan Aminiya ya ba ni dama in yi ga Mai girma Gwmanan Jihar Zamfara kan lallai ya kula da harkar ilimi, musamman biyan kudin jarabawar NECO da WAEC da JAMBa, ga ‘’yan asalin wannan jiha ta mu mai albarka. Domin wannan ita ce kafa daya tilo da za mu iya kira, […]

Gwamnan Zamfara ka biya wa dalibai kudin jarabawa
Gwamnan Zamfara ka biya wa dalibai kudin jarabawa

Kai tsaye nike son Editan Aminiya ya ba ni dama in yi ga Mai girma Gwmanan Jihar Zamfara kan lallai ya kula da harkar ilimi, musamman biyan kudin jarabawar NECO da WAEC da JAMBa, ga ‘’yan asalin wannan jiha ta mu mai albarka. Domin wannan ita ce kafa daya tilo da za mu iya kira, har kukanmu ya kai ga kunnuwan gwamna. 

Hakika akwai bukatar in yi matashiyua zan so ya mai girma jagoran Zamfara ka yi tuni da cewa; duk dunbin dukiyar da ke hannunka a halin yanzu mallakar talakawan Zamfara ce, alfanunta a hannunka ka amfanar da Zamfarawa da ita ta hanyar da; za su ginu akan turba ta gari. Abin da ya fi kyau ka fi mayar da hankali\wajen ganin cewa dukiyar Jihar Zamfara ta amfani Zamfarawa.
A nawa dan gajeren tunanin zan iya cewa ba wani fanni da ya fi dacewa, ka mayar da hankali a kansa kamar ilimi, wanda masana harshen Hausa ke kira da “gishirin zaman duniya,” a wani fannin suka kira shi da; “haske.” Kasancewar tun da Allah ya damka maka jagorancinmu, mun ga take-takenka a kan hakan.
Don haka kai tsaye zan so in yi magana ne akan fanni daya, domin “idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai” kuma wannan dan takaitaccen shafi ba zai isa, in zayyano komai akan matsalar da fannin ilimi a Jihar Zamfara ke fuskatan ba.
Fannin da zan dauka kuwa shi ne daliban da a kowace shekara suke zana jarabawar kare babbar makarantar sakandare, amma kamin sakamakon nasu ya fito sai an kai ruwa rana, rayuwar dalibai ta kai matuka wajen baci, saboda da zaman jira. Kamar kowace shekara, wannan shekarar tamkar wadda ta gabaceta, domin yanzu haka duk da irin dogon lokacin da aka dauka da sako sakamakon jarabawar WAEC DA NECO.
A makarantu masu zaman kansu, ‘ya’yan masu gida a tsakar rana har yanzu suna nan su na zaman jiran gawon shanu, duk da cewa a rana daya ne ake rubuta jarabawar tsakanin makarantu masu zaman kansu da na gwamnatin.
Tabbas mun yi zaman jira, tare da yi ma uzuri, domin mu ga iya gudun ruwanka, ko da za ka dauki matakin biyan kudin, wanda zai sa hukumomin shirya jarabawar su sako jarabawar, amma har yanzu ga shi an wayi gari; manyan makarantun da dama a ciki da wajen jihar nan tamu sun yi jarabawar share fagen shiga, jami’o’i da kwalejojin kimiyya da Fasaha da kwalejojin ilimi, na jiha da na tarayya. Babbar damar dan talaka a Jihar Zamfara, ita ce, ya nemi gurbin karo ilimi a Maru (COE MARU), kasancewar ita ce makaranta mai dan sauki ga ‘ya’yan talakawa. Yau, an wayi gari su ma din sun gaji da jiran gwamnatin jiha, su biya kudin har sun ga ji.
A ranar 19-11-2014, sun yi shirya jarabawa a matakin farko, wanda abin takaici ba wata karamar hukuma da ta cika ajin da aka tanadar wa ‘ya’yanta, domin zana jarabawar, har Gusau babban Birnin jiha, da a duk shekara ba wani aji da ke dauke dalibansu. Amma abin haushin daga wasu jihohin, wajen da aka tanadar musu ko dauke su bai yi ba. Wannan abin kunyar har ina? A zo cikin gidanka, a fi ka taka rawa!
Duk da haka har yanzu ba wani motsi da ‘ya’yan talakawa suka ga gwamnatinka na yi don ganin cewa; gwamnatinka ta biya wadannan kudi, domin su ma ‘ya’yan talakawan su samu damar wucewa makaranta, domin zurfafa karatunsu. Kasancewar dukkan mutun mai kishin kansa, to fa yana son ya zama mai amfani ga kansa, danginsa, da al’ummarsa ba ki daya. Don haka hanya daya tilo da zai bi ya cimma wannan kuduri shi ne, ya tashi ya nemi ilmin ta yadda zai yada masa hanya, ya hango mafita.
Duk yadda Allah ya halitto ka dole ka gode masa, tabbas mu talakawa ne, kuma muna godiya ga Allah da ya sa kowa a mutun. Don haka kai kanka, da bazarmu kake taka rawa. Ko da yanzu ka iya cewa; an ci moriyar ganga ne an yarda da kwaurenta, to ga lokacin amfanin gangar nan ya taso, domin yanzu haka har kun daukota kun kwankwasa, har kun fara buga sautinta ya fara amo.
Shawararmu a gareka ka yi gaugawar debo kudi cikin asusun jiha, kasancewar ba wai kudin wasu mutane ne daban ba. A’a, kudin al’ummar da kake jagoranta ne. Don amfaninsu, gare su shi ne ka debo su ka biya masu bukatunsu.
Daga karshe muke rokon Allah ya sa kiranmu ya iya a kunnuwanka, kai kuma ka amsa kiranmu, ta hanyar biyan kudin cikin lokaci. Su kuma dalibban muna yi musu fatan Allah ya datar da su da sakamako nagari, ya ba su ikon wucewa su zurfafa karatunsu. Ya Allah ka sa karatun ya amfani al’ummar Zamfara da Najeriya, da rayuwarsu baki daya.
Abdulmalik Saidu mai biredi tashar bagu, Gusau (jami’in hulda da jama’a na kungiyar Muryar Talaka reshen jahar Zamfara) 08069807496.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi