Za A Bi Kadun Kisan Sheikh Abubakar Mada — Gwamna Dare
Wani mazaunin garin ya bayyana kisan Imam Abubakar Mada a matsayin wani abu mai kama da siyasa ko bita da ƙulli.
Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Dauda Lawal Dare, ya lashi takobin bin kadun kisan Malam Abubakar Hassan Mada da ake zargi rundunar tsaro ta gwamnatin jihar ta hallaka.
Gwamnan ya sha wannan alwashi ne yayin da yaje ta’aziyyar marigayi Sheikh Mada, inda ya jajanta wa iyalai, ƴan uwa da kuma dangin malamin.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa Gwamna Lawal ya yi sallar Juma’a a masallacin Mada.
Yayin wannan ziyarar, gwamnan ya yi ta’aziyya ga iyalan marigayi Malam Abubakar Hassan Mada, hakimin gundumar, da sauran al’ummar yankin.
Da yake jawabi bayan idar da Sallar Juma’a, Gwamna Lawal ya tabbatar wa al’ummar garin Mada cewa, za a yi adalci a kan faruwar lamarin.
Ya ce, “Na zo nan ne domin in tabbatar wa mutanen garin Mada cewa, gwamnatina ta himmatu wurin ganin an tabbatar da adalci tare da hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.
- Muna Fargabar Za A Samu Hare-Hare A Wuraren Tarukan Jama’a — DSS
- A bai wa mata jagorancin Nijeriya saboda maza sun gaza — PDP
“Babu wanda za a bari ya ci bulus, muddin bincike ya tabbatar da cewa yana da hannu wurin kisan Malam Abubakar, to dole sai ya fuskanci hukunci.
“Za mu yi duk mai yiwuwa wurin tabbatar da cewa an bi kadun jinin marigayi, kuma an yi wa iyalansa adalcin da ya kamata.”
Gwamnan ya bayyana cewa, lokacin da wannan mummunan al’amari ya faru ba ya gari, amma tun kafin ya dawo ya bai wa hukumomin tsaro a jihar umarnin fara bincike domin tabbatar da an kamo waɗanda suka kashe malamin saboda a gaggauta hukunta su.
Ana zargin waɗanda suka kashe Malam Abubakar da zarginsa cewa ya taba ceton waɗansu da aka taba kamawa da hannu a garkuwa da mutane a wani lokaci can baya.
Tuni dai kungiyoyi da jama’a kusan ko’ina a faɗin ƙasar suka bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda aka yi wa malamin kisan gilla ba tare da an kaishi kotu, an yanke masa hukunci kan abin da ake zargin ya aikata ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, ana zargin jami’an tsaron sa-kai na Gwamnatin Zamfara (CPG) da aka fi sani da Askarawan Zamafar sun yi wa Babban Limamin Masallacin Juma’a na garin Mada, Imam Abubakar Hassan, yankan rago.
Wata majiya mai kusanci da marigayin ta ce jami’an sa-kai biyar ne suka zo ƙauyen Mada da ke Karamar Hukumar Gusau a kan babura suka ɗauki marigayin bayan sallar La’asar ranar Lahadi.
“Lokacin da suka kama shi, mun yi tunanin ana gayyatar sa ne kan wata magana ko don gudanar da bincike, amma sai muka tsinci gawarsa an jefar a bayan gari.
Wani mazaunin garin, Muhammad Yunus ya bayyana kisan babban limamin a matsayin wani abu mai kama da siyasa ko bita da ƙulli.
Ya ce, Malam ya taba tsaya wa wadansu matasa biyu da ’yan banga suka kama bisa zargin su da hannu a fashi a bara.
“Na yi imanin wannan abin ne ya sa ’yan bangar, suka kashe Imam.
Babban Kwamandan ’Yan Sa-Kai na Jihar Zamfara, Kanar Rabi’u ’Yandoto ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, kawo yanzu abin da aka iya ganowa shi ne ’yan sa-kai na zargin sa da taimaka wa masu garkuwa da mutane da satar shanu.
Kanar ’Yandoto ya bayyana cewa, hedikwatar CPG ba ta san komai game da kamun da aka yi wa babban limamin ba, inda ya ƙara da cewa “a ka’ida, idan muna zargin mutum muna kamo shi ne domin bincike, ba kashewa ba.
“Don haka, wannan kisa ba bisa ka’ida aka yi sa ba, an aikata haramun kuma za a yi bincike.
“Ba mu ba jami’anmu umarnin kama kowa ba, don a yanzu haka jami’an CPG biyu da ake zargi da kisan babban limamin suna hannunmu; daga Mada aka kawo su kuma za mu yi musu tambayoyi bisa zargin da ake musu.”