Gwamnan Zamfara ya hana magoya bayansa daukar makami a wajen yakin neman zabe

Gwamanan jJihar Zamfara Alhaji Abdul,aziz Yari Abubakar ya ja kunnen magoya bayan sa, musamman ma matasa da kada wanda aka sake gani da makami a lokacin da ake yaakkin neman zabe, domin a haka zas u sake cin zabe a shekara ta 2015.Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa ga […]

Gwamnan Zamfara ya hana magoya bayansa daukar makami a wajen yakin neman zabe
Gwamnan Zamfara ya hana magoya bayansa daukar makami a wajen yakin neman zabe

Gwamanan jJihar Zamfara Alhaji Abdul,aziz Yari Abubakar ya ja kunnen magoya bayan sa, musamman ma matasa da kada wanda aka sake gani da makami a lokacin da ake yaakkin neman zabe, domin a haka zas u sake cin zabe a shekara ta 2015.
Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa ga dubban jama’ar da suka taru don raka shi ya maida takardar takararsa da ya saya .
Ya ce yana so duk jami’an tsaro su sanya idanu kan wadanda suke yawo  da makamai, domin a cewarsa ba ya son ganin wani ko wasu ko wata sun rasa rayukansu kan hanyar sake cin zabensa.
Gwamnan ya kara da cewa haka nan kuma ba shi da bukatar a ce ya zama sanadiyyar wani ya rasa wani bangare na jikinsa saboda shi, ma’ana ko wani ya rasa idanu ko hannu ko kafa.
Da ya koma kan abokan adawarsa kuwa, ya ce wasu suna ta kokarin ganin gwamnatin tarayya ba ta biya shi bashin da yake binta ba, kamar yadda ta yi  alkawari kan aikin hanyar da ya gabata a jihar wadanda suke na gwamnatin tarayya ne. Ya ce wadannan suna aikin banza ne, domin a cewarsa Allah ya fi su. Ya ce gwamnatin tarayya ta rike kudinta, don Allah zai ba shi wadanda za su yi yakin neman zabe da su.
Da ya koma kan maganar tsaro da  wasu ke amfani da ita don zaginsu, ya ce, kowa yasan yadda Gwamnatin  Jihar Zamfara da jami’an tsaro suka hana idanuwansu barci  babu dare, babu rana, don ganin sun kawo karshen yawan kashe-kashen da ke faruwa a cikin jihar.
Gwamnan ya kara da cewa in Allah ya yarda matukar suka kafa gwamnati a kasar nan, to jami’an tsaro za su dara, domin a cewarsa za a daina samun wasu da ake kira boko haram suna fada wa barikinsu, suna korar su, saboda rashin kayan aiki.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron kwamandar yakin neman zabensa, Alhaji  Ibrahim Nabature,  ya nemi gwamnan ne da ya yi kokari ya karasa sauran ayyukan da suka rage masa na hanya, wadanda ba su wuce kashi goma10 ba .
Nabature ya kuma nemi Gwamnan  Jihar Alhaji AbdulAziz Yari da ya yi kokari idan ya sake komawa kan mulki ya share wa al’ummar Jihar Zamfara hawaye kan matsalar da suke da ita na rashin filin jirgin sama, saboda ganin yadda ake jigila da alhazansu idan lokacin aikin Hajji ya yi, na daukarsa daga Gusau zuwa Sakkwato, domin kawai su hau jirgi, inda ya ce wannan matsalar tana matukar ci musu tuwo a kwarya, domin a cewarsa a cikin jihohin da aka yi tare da jihar Zamfara  babu wadanda ba su da filin jirgin sama.