Gwamnan Zamfara ya roki jama’ar jihar su taimaka wa jami’an tsaro
Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari Abubakar ya nemi al’ummar jihar su tashi tsaye wajen taimaka wa gwamnati wajen shawo kan matsalar tsaron da ake fama da ita a wasu kananan hukumomin jihar.Gwamna Abdul’aziz Yari ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a makon jiya, inda ya ce gwamnatinsa tana […]
Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari Abubakar ya nemi al’ummar jihar su tashi tsaye wajen taimaka wa gwamnati wajen shawo kan matsalar tsaron da ake fama da ita a wasu kananan hukumomin jihar.
Gwamna Abdul’aziz Yari ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a makon jiya, inda ya ce gwamnatinsa tana neman al’umma su taimaka wa jami’an tsaro wajen sanar da su duk wani abin da ba su gane ba, domin gwamnati ita kadai ba za ta iya magance wannan matsala ba sai da taimakon al’umma.
Gwamnan ya ce ya dace jama’a su sanar da jami’an tsaro duk wani bakon abu da ya zo musu ko wanda ba su yarda da shi ba.
Gwamna Yari ya ce sun yi zaman gaggawa a tsakanin gwamnonin Katsina da Sakkwato da Kebbi da Kaduna da kuma Neja don samar da hanyar da za a kawo karshen wannan
matsala ta rashin tsaro.
Ya ce gwamnatinsa ta tashi tsaye don samar da hanyar kawo karshen ta’addancin da ake yi a jihar.
Idan ba a manta ba a cikin azumi wasu mahara sun kashe mutane da dama a karamar Hukumar Binin Magaji, wanda hakan ya jawo yin gudun hijira ga wasu mutane masu yawa zuwa cikin garin Birnin Magaji da garin Dauran da kauran Namoda da ke
karamar Hukmar kauran Namoda.