Gwamnan Zamfara ya umarci a rushe gidajen da babu su a ka’ida
A zagayen da gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar yake yi a cikin jihar, don gane wa idanuwansa yadda aikin hanyar da ya bada yake tafiya, ya ba da umurnin a rushe gidajen da za su kawo wa aikin tarnaki, musamman wadanda suka yi kunnen uwar shegu da umurnin da aka ba su,Gwamna Yari ya […]
A zagayen da gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar yake yi a cikin jihar, don gane wa idanuwansa yadda aikin hanyar da ya bada yake tafiya, ya ba da umurnin a rushe gidajen da za su kawo wa aikin tarnaki, musamman wadanda suka yi kunnen uwar shegu da umurnin da aka ba su,
Gwamna Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci hanyar da ta tashi daga masallacin Muslim Foundation zuwa asibitin Shagari, wanda aka bai wa kamfanin SKY tun a shekarar 2011.
Sai dai zagayen ya bata wa gwamnan rai matuka, saboda yadda aikin yake tafiyar hawainiya, da kuma ganin yadda masu lura da aikin ke yi wa aikin rikon sakainar kashi.
Sai dai gwamnan ya umarci kamfanin da ya tabbatar an kammala aikin a lokacin da aka kayyade, wato zuwa 30 ga watan 12.
Idan ba a manta ba, gwamnati ta ba da wannan aiki ne kan kudi sama da Naira miliyan 300, kuma hanyar ta fara ne daga Muslim Foundation zuwa Tullukawa, har zuwa asibitin Shagari.
Ita kuwa hanyar da ta fara daga asibitin Shagari zuwa sabon gari, har ta kai Bello Bara’u an ba da ita ne ga kamfanin nan na Habib Enginering, wanda a halin da ake ciki sun kammala aikin.
Gwamnatin AbdulAziz Yari dai ta ba da ayyukan hanyoyin cikin garin Gusau kawai kan kudi Naira Biliyan 300 da Dubu 600, kuma ana nan ana ci gaba da ayyukan.