Gwamnan Zamfara ya zargi kwamishinoni da nuna halin ko-in-kula

Gwamnati tana kashe sama da Naira miliyan 360 a wata don gudanar da ayyukan yau da kullum ga kwamishinoni, saboda haka da mamaki idan kwamishina ya kasa sayen na’ura mai kwakwalwa don amfanin ofishinsa.Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar ne ya bayyana haka, cikin bacin rai, a makon jiya a gaban dubban jama’a, wajen […]

Gwamnan Zamfara ya zargi kwamishinoni da nuna halin ko-in-kula
Gwamnan Zamfara ya zargi kwamishinoni da nuna halin ko-in-kula

Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari AbubakarGwamnati tana kashe sama da Naira miliyan 360 a wata don gudanar da ayyukan yau da kullum ga kwamishinoni, saboda haka da mamaki idan kwamishina ya kasa sayen na’ura mai kwakwalwa don amfanin ofishinsa.
Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar ne ya bayyana haka, cikin bacin rai, a makon jiya a gaban dubban jama’a, wajen jin sakamakon da kwamitin binciken matsalolin makarantun sakandare da ya kafa, a karkashin jagorancin Farfesa Tukur Adamu, malami a Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato, ya gabatar masa.
Gwamnan ya kara da cewa, “Ni da ku mun yi imani da Allah da Ranar Lahira, kuma mun yi imanin za a tashe mu, bayan mun mutu, kuma mun yi imanin za mu yi bayanin kowane kobo da muke kashewa, daya bayan daya,  don haka mu ji tsoron gamuwarmu da Allah.
“A lokacin da wannan gwamnati ta zo, ta samu ana kashe Naira miliyan 270 a wata, amma don komai ya tafi daidai kuma don kada a sami matsala, sai muka maida kudin suka zama Naira miliyan 360, amma ko na’ura mai kwakwalwa ba za a iya saye don gudanar da aikin ofis ba?”
Ya kara da cewa, “Da muka hau kan madafun iko, mun ba da na’ura mai kwakwalwa sama da saba’in, yanzu babu ko daya ,to duk ina suke? A ji tsoron Allah.  Wannan matsala ce ta kowa da kowa kuma matsala babba, fiye da yadda wasu suke daukarta kuma wasu suna daukar cewa wannan ba matsalarsu ba ce ko kuma wannan ba aikinsu ba ne, aikin wancan ne, ba haka abin yake ba ko kadan”.
Gwamna Yari ya ce, “Idan muka koma bangaren abinci, kamar yadda Farfesa yake fadi, ku dubi sakamakon da yaranmu suke fitowa da shi. Sakamakon yunwa da suke fama da ita. Me mutum zai iya gudanarwa, idan bai ci abinci ba, balle a ce ma karatu? Ai ba zai yiwu ba. To dole mu gyara ko da abin ba zai yi wa wasu dadi ba, kuma za mu dauki shawarar da kwamitin za su fito da shi, mu yi amfani da shi ko da ran kowa zai baci”.
Wadannan bayanai sun biyo bayan matsalolin da kwamitin ya fitar ne, wadanda suka shafi rashin kayan aiki da rashin isasshen abinci ga dalibai da rashin guraren ba haya da wurin kwana da rashin ajujuwa da kuma matsalar kwararrun malamai da kuma karancin malaman kansu da kuma cunkoson dalibai a cikin ajujuwa da dai sauransu.
Binciken wakilinmu ya nuna, wannan lamari bai yi wa wasu jami’ai dadi ba, musamman yadda gwamna ya dora laifin faruwarsa kan mafiya yawan ma’aikatan makarantu tun daga malamai da shuwagabanni da masu kula da ci-maka da masu shirya cuta da dai sauransu, balle uwa-uba kwamishinoni da gwamnan ya bayyana abin gwamnatinsa ke kashe wa ofisoshinsu a wata.