Gwamnati ce ta lalata harkar fim – Abba Al-Mustapha
Gwamnati ce ta lalata harkar fim – Abba Al-Mustapha
Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood kuma dan siyasa a jam’iyyar NNPP, Abba Al-Mustapha, ya ce gwamnati ce ta lalata harkar fina-finan Kannywood.
Almustapha ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da gidan rediyoon Freedom da ke Kano, inda ya ce rashin tallafa musu da gwamnatin ta yi ya sanya sana’ar ta fadi kasa warwas.
- Rashin tabbas kan sadaki ya kawo tsaiko a shari’ar raba auren ’yar Ganduje
- Malaman makaranta sun fara yajin aiki a Ingila kan karin albashi
“Su waye suka lalata harkar fim? Gwamnati!! Ina kudi yake a cikin harkar fim? Ai babu!
“Kamata ya yi gwamnatin ta ba da tallafi tunda ‘ya’yanta ne, domin masana’antar a karkashinta take. Ko baki san akwai hukuma ta tace fina-finai da ta hakkin mallaka ba ne?
“To me ya sa da aka samu matsalolin kudi ba ta shigo ba? Me ya sa duk ba za ta zo ta ba mu jari ba? Yanzu kamar ni ai ina bukatar ka bani tallafi na yi ingantattun series (finafinai masu dogon zango) don kara bunkasa harshenmu, da addininmu da sauransu. Kamar yadda za a tallafa wa manomi haka dan fim. Saboda masana’anta fa aka kira ta!” in ji Al-Mustapha.
Jarumin ya kuma ce baya ga wadannan dalilai ma, idan gwamnatin na bukatar a tallata ta, ‘yan fim din take nema.