‘Gwamnati da malamai sun jefa jama’ar Kano cikin hadari’
Wasu masana sun zargi gwamnati da limaman Kano da jefa rayukan al’ummar jihar cikin hadari ta hanyar bayar da umarnin gudanarwa da kuma jagorantar Sallar Idi ba tare da bin shawarwarin kwararru a harkar lafiya ba. Da ma dai wasu masana sun nuna rashin gamsuwa da matakin da gwamnatoci a wasu jihohi suka dauka na […]
Wasu masana sun zargi gwamnati da limaman Kano da jefa rayukan al’ummar jihar cikin hadari ta hanyar bayar da umarnin gudanarwa da kuma jagorantar Sallar Idi ba tare da bin shawarwarin kwararru a harkar lafiya ba.
Da ma dai wasu masana sun nuna rashin gamsuwa da matakin da gwamnatoci a wasu jihohi suka dauka na bayar da damar yin Sallar Juma’a da ta Idi, suna gargadin cewa bai kamata ba.
Tsohon shugaban Hukumar Kula Da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, na cikin masanan da ke da wannan ra’ayi.
An tafka kuskure
A cewar Farfesa Yusuf, gwamnati, musamman masu rike da mukaman siyasa sun hada kai da malaman addini wajen karya dokokin lafiya duk kuwa da cewa sun san illar da ke tattare da hakan.
- Yadda aka saba dokar tazara yayin Sallar Idi a Kano
- ‘Ban yafe wa masu cewa na kawo coronavirus Kano ba’
“Kowa ya riga ya san illar da ke tattare da hakan. Da ni da kai da kowa da kowa ya sani kamar yadda muka sha yin bayani a baya, amma gwamnati da malamai [a jihar Kano] suka hada kai duk da sun san illar don kawai su faranta wa jama’a rai – duk da sanin illar da ke tattare da cunkoso a wannan lokacin.
“Mun sha yin bayani kan yadda cutar nan ke saurin yaduwa a tsakanin mutane kamar wutar daji musamman idan suka shiga cunkoso.
“Ko a Musulunce ai ba a yarda mutum ya jefa kansa cikin abin da karara ya san hadari ba ne; kawai sai dai Allah ya kare mu amma kuskure dai an tafka”, inji Farfesa Yusuf.
Masanin ya kuma yi takaicin yadda kowanne sashe na al’umma ya yi kunnen uwar-shegu da shawarwarin, yana mai gargadi kan illar da ka iya biyo baya.
Ko a kwanakin baya dai yayin wata tattaunawa da Aminiya, wani kwararre kan cututtuka masu yaduwa kuma Shugaban Hukumar yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Yankin Afirka ta Yamma, Farfesa Abdulsalam Nasidi, ya yi gargadin cewar muddin aka ci gaba da watsi da shawarwarin masana harkar lafiya, to tabbas akwai yiwuwar harsashen da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kan cewa cutar na iya dawwama har illa masha Allah.
Rahotanni dai sun rawaito yadda aka gudanar da Sallar Idi a wasu wurare a jihar Kano kamar yadda aka saba yi a baya ba tare da ba da tazara ko yin amfani da kyallen rufe fuska ba.
Wasu malamai ma
Baya ga wasu masana, a cikin malamai akwai wadanda suka yi ta suka tun bayan da gwamnatin jihar ta Kano ta bayar da sanarwar sahale wa alumma su gudanar da Sallar Idi, suna cewa ta yi azarbani wajen daukar wancan mataki duba da cewa jihar ce ta biyu a jerin jihohin da ke da yawan wadanda suka kamu da coronavirus a fadin Najeriya.
A wancan lokaci Majalisar Malamai ta Jihar Kano a karkashin jagorancin Shaikh Ibrahim Khalil ta ga beken gwamnatin ta Kano a kan wannan mataki da ta dauka inda ta yi kira da kakkausar murya da a janye wancan matsayin don gudun jefa rayuwar alumma cikin hadarin kamuwa da cutar ta kurona.
Sai dai gwamnatin ta yi fatali da kiraye kirayen da aka yi ta yi mata, ta kuma ci gaba da shirye-shiryen tunkarar Sallar Idin.
Gwamnatin ta fitar da wasu ka’idoji ga masu zuwa sallar wadanda ta.ce wajibi ne a kiyaye su.
Matsayin gwamnati
A sanarwar da ta fitar ta bakin Kwamishinan Watsa Labarai Kwamared Muhammad Garba, gwamnatin ta bayyana cewa dole ne masu zuwa Sallar Idi su sanya takunkumin rufe fuska tare da bayar da tazara a tsakaninsu.
A cewar gwamnatin ta kafa kwamiti a karkashin jagorancin Kwamishinan Muhalli Dokta Kabir Ibrahim Getso wanda ta dora wa alhakin raba kayayyakin kariya a masallatai tare da tabbatar da cewa masallatan sun yi amfani da kayayyakin.
Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa jama’ar da suka fita Sallar Idin ba su bi wadancan dokoki da gwamnatin ta shimfida ba – ba su sanya takunkumin rufe fuska ba haka kuma ba su bayar da tazara a tsakaninsu ba.
‘Ba laifinmu ba ne’
To sai dai kuma a daidai lokacin da ake ta nuna musu yatsa kan cewa su ne da laifi, wasu limaman sun ce ba su suka kar zomon ba.
A tattaunawarsa da Aminiya, daya daga cikin limaman da suka jagoranci Sallar Idin a daya daga cikin masallatan dake cikin birnin Kano wanda bai so mu bayyana sunansa ba ya ce limamai ba su da laifi a cikin lamarin kwata-kwata.
A cewarsa, hakkin sakawa da kuma tabbatar da bin kowacce doka nauyi ne da rataya a wuyan hukumomi amma ba limamai da malamai ba.
“Mu a matsayinmu, abin da kawai za mu iya yi shi ne mu wa’azantar da jama’a kan abin da Allah da manzonsa suka ce, sannan idan akwai wata doka da gwamnati ta saka mu kan iya fadakar da jama’a a kai.
Hakkin tursasawa
“Amma hakkin tabbatarwa ko tursasa su su bi dokar wannan sai gwamnati.
“Kamar yadda kuka gani da idanunku gwamnati ba ta yi wani hobbasa ba wajen ganin ta tilasta jama’a a kan haka.
“Abin da kawai gwamnati ta yi shi ne ta kawo man tsaftace hannu na sanitizer don mu fesa wa wadanda suka zo sallah, shi din ma ba kowa ne ya samu ba”, in ji limamin.
Ya kara da cewa suna goyon bayan batun bayar da tazara, wanke hannu a-kai-a-kai da sanya kyallen rufe fuska da sauran matakan kariya daga kamuwa da cutar kamar yadda masana harkar lafiya suka bayar da shawara don takaita yaduwar cutar.
Rawar gwamnati
Aminiya ta tuntubi Kwamishinan Harkokin Addinai na jihar wanda kuma mamba ne a kwamitin tabbatar da cewa an bi ka’idojin, Dokta Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible), a kan yadda aka haihu a ragaya.
Shi kuma ya dora alhakin faruwar hakan a kan rashin wadatuwar kayayyakin kariyar a wajen jama’a.
“Idan kin duba kayayyakin da muka samu ba su fi miliyan biyu ba; ta yaya za a yi su wadaci al’umma mai mutane sama da miliyan 14?
“Duk da cewar gwamnatin ta samar da kayayyakin kariyar ga jama’ar jihar sai dai kayayyakin ba su isa ba saboda yawan mutane.
“Akwai ma masallatan da ba su samu kayan ba kwata-kwata. Amma insha Allah za a samar da kayayyakin isassu”, inji Baba Impossible.
A cewarsa gwamnati tana bin matakai kafin ta zartar da hukunci.
Wani hanzari
“Duk da cewa mun wajabta amfani da takunkumi amma dole sai an bi wasu matakai da suka hada da wayar da kai domin har yanzu kashi 70 cikin 100 na al’ummar jihar ba su ma yarda akwai cutar ba”.
Sai dai kwamishinan bai yi bayani a kan dalilin da ya sa gwamnati ta ba da damar a fita sallar ba tun da ta san ba ta da halin tabbatar da bin ka’idojin da ta shimfida.
A yanzu dai jihar Kano c eke bin Legas a yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da corona virus a Najeriya kamar yadda alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC suka nuna.
A cewar NCDC, zuwa tsakar daren Litinin addain wadanda aka tabbatar sun kamu a jihar ya kai 919.