Gwamnati ga ’yan Najeriya: Ku kara hakuri bayan wuya sai dadi

Gwamnatin Tarayya ta bukaci ’yan Najeriya su kara hakuri dangane da wahalhalun da suke fuskanta na karancin man fetur da rashin wutar lantarki, inda ta ce tana aiki ba kamma hannun yaro domin kawo musu sauki.Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci hekdwatar Kamfanin Media Trust Ltd mai […]

Gwamnati ga ’yan Najeriya: Ku kara hakuri bayan wuya sai dadi
Gwamnati ga ’yan Najeriya: Ku kara hakuri bayan wuya sai dadi

Gwamnatin Tarayya ta bukaci ’yan Najeriya su kara hakuri dangane da wahalhalun da suke fuskanta na karancin man fetur da rashin wutar lantarki, inda ta ce tana aiki ba kamma hannun yaro domin kawo musu sauki.
Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci hekdwatar Kamfanin Media Trust Ltd mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya a Abuja, inda ya ce gwamnati tana tausaya wa ’yan Najeriya tare da damuwa da halin da suke ciki, inda ya ce kokarin gwamnatin zai haifar da da mai ido tare da kawo dadi ga ’yan Najeriya.
“A matsayinta na gwamnatin da ta hau gadon mulki bisa karfin ikon jama’a, muna jin zafin halin da jama’a ke ciki kuma muna matukar tausaya musu. Sakonmu ga ’yan uwanmu ’yan Najeriya shi ne wannan gwamnati a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari tana aiki wurjanjan domin saukaka wahalhalun da ’yan Najeriya ke ciki, kuma nan da dan wani lokaci ’yan Najeriya za su fara jin dadi,” inji Ministan.
Alhaji Lai  Mohammed ya ce gwamnati tana sane cewa ’yan Najeriya sun fara tababa kan gaskiyar canjin da take fada tana yi, “Mun lura da shakkun da wasu ’yan Najeriya ke yi kan anya wannan ne canjin da suka jefa wa kuri’a. Ina shaida wa ’yan Najeriya cewa shirinmu na canji da gaske ne kuma ’yan Najeriya sun yi kusa su samu canjin da suka zaba,” inji Ministan.
Game da halin da ake ciki game da man fetur, Ministan ya ce an dauki matakai na gaggawa domin kawo karshen karancin man, yayin da ake ta kokarin samar da hanyar rabuwa da wahalar mai na dindindin.
“Kamfanin Mai na kasa (NNPC) yana dada samarwa da rarraba wadataccen man fetur ga sassan kasar nan, amma yawan zuwa gidajen mai da bashin da ake bi suna jawo wahala jama’a su samu sauki nan take. Kuma ana dada sanya ido domin ganin ana sayar da man a kan farashin gwamnati. Kuma keta dokar farashin ko boye man laifuffuka ne da suke dauke da hukunci, ciki har da rarraba man kyauta ga jama’a da rufe gidajen man da aka samu da boye man da biyan tara da kuma kwace lasisin dan kasuwar,” inji shi.
Minista Mohammed ya ce a mataki na tsakiya wahalar da ake samu ta canjin kudaden kasashen waje an magance ta ta hadin hannu da Babban Bankin Najeriya inda aka samo hanyoyin cike gibin da ake samu wajen samun kudaden musaya. Ya dora laifin karancin wutar lantarki kan rashin samar da gas ga janaretocin tashoshin wutar lantarki, inda ya ce Kamfanin NNPC yana nemo wasu hanyoyi na samar da gas bayan da harin da aka kai ga bututun mai na Forcardos Edport ya tilsta dakatar da tura gas ga tashoshin.
Da ya juya kan asusun musamman na Naira biliyan 500 da gwamnati ta amince da shi, ya ce wannan shiri zai fitar da dimbin ’yan Najeriya daga cikin talauci. Ya ce ta hanyar amincewa da kasafin kudin bana, gwamnati ta shirya farfado da tattalin arzikin kasa tare da farfado da aiki a wuraren da aka fara su a baya musamman hanyoyi da gine-gine.
Ya bayyana muhimman sassa shida da tallafin zai shafa da suka hada da daukar wadanda suka kammala jami’a dubu 500 don horar da su aikin koyarwa da bayar da horo ga wadanda ba su yi jami’a ba su dubu 370 da daukarsu aiki da kuma horar da ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu miliyan daya tare da ba su basussuka.
Sauran su ne shirin ciyar da daliban firamaren aji 1 zuwa 3 da tallafa wa gajiyayyu musamman a yankunan karkara da bayar da tallafin karatu ga daliban da suke nazarin kimiyya da kere-kere da injiniya da lissafi.