Gwamnati ki shiga tsakaninmu da masu karbar kudin shiga a kasuwa – Ikechuku
Wani dan kasuwa kuma sakataren kasuwar albasa da wake a layin Legos da ke cikin garin Benin, mai suna Ifrehme Ikechuku, ya bayyana cewa daga cikin matsalolin da ’yan kasuwar albasan ke fama da su akwai batun masu bayar da tikitin karbar kudi a kasuwar wadannan ke matsa wa ’yan kasuwarmu, tare da nuna rashin […]
Wani dan kasuwa kuma sakataren kasuwar albasa da wake a layin Legos da ke cikin garin Benin, mai suna Ifrehme Ikechuku, ya bayyana cewa daga cikin matsalolin da ’yan kasuwar albasan ke fama da su akwai batun masu bayar da tikitin karbar kudi a kasuwar wadannan ke matsa wa ’yan kasuwarmu, tare da nuna rashin mutunci.
Ya ce ina rokon Gwamnatin Jihar Edo ta taimaka ta tsawata wa irin wadannan jagudoji su daina musguna wa ’yan kasuwarmu da sunan bada tiketin karbar kudin shiga, kuma muna bukatar matakan tsaro daga ita gwamnatin jihar, domin kare lafiyarmu da rayukanmu, tare da dukiyarmu a kasuwar.
Game da batun rashin ciniki kuwa, Ikechuku ya ce, ‘a lokutan baya muna samun ciniki, amma yanzu abin ya canja gaba daya, don haka akwai matsalar rashin ciniki a irin kayan da muke sayowa daga Arewa mu kawo, mu a wannan kasuwar ta albasa da wake da dankalin gida da sauran wasu kayan amfanin gona na Arewa, domin mutane suna kokawa a kan babu kudi. Wannan lamarin ya janyo mana rashin ciniki.’
A cewarsa, hatta a makon da aka gudanar da bukukuwan sallah da muka sa rai za mu samu mu rage kayan da ke hannun abin ya bi ya kulle gaba daya, amma duk da haka muna gode wa Allah, domin samun kadan ya fi a ce babu kwata-kwata.
Kuma abin da nake son in fada wa ’yan uwana ’yan kasuwar mu da sauran muane baki daya, ya kamata mu rika yin hakuri da juna, tare da godiyar Allah akan abin da ake samu na alheri cikin kasuwa, saboda kowa ya san yanayin kasar nan, yanzu akwai rashin kudi.
“Gwamnati ta tsuke bakin aljihunta, kudi ba ya kaiwa hannun talakawa, ga kuma zabe yana karatowa ko mene ne za su gaya wa talaka? Ba mu sani ba,” inji shi.