Gwamnati na asarar biliyan 10 a kullum sakamakon cunkoson Apapa-Dangote
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce Gwamnatin Tarayya tana asarar fiye da Dala biliyan 10 a kullum sakamakon cunkoson tashar sauke kaya ta Wharf da ke unguwar Apapa. Dangote ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala taron gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu wanda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta. […]
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce Gwamnatin Tarayya tana asarar fiye da Dala biliyan 10 a kullum sakamakon cunkoson tashar sauke kaya ta Wharf da ke unguwar Apapa.
Dangote ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala taron gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu wanda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Dangote zai kammala sake ginin hanyar Apapa zuwa tashar Wharf a watan Yuni na shekarar 2018.
Da yke yin karin bayani ga manema labarai a fadar shugaban kasa, Dangote ya ce “Za mu fara aikin Apapa zuwa yankin Oworonshoki a mako mai zuwa kuma tuni muka mika komai da suka hada da tsarin hanyar ga masu aikin. Saboda haka za mu fara aiki mako mai zuwa”.