Gwamnati na bukatar tsaffin ma’aikata don yi mata jagora – Shugaban ‘Yan Fansho
Aminiya: Me za ka bayyana mana a kan irin halin da wannan kungiya take ciki? Daura: Alhamdulillahi! Wannan kungiya tana cikin hali mai kyau, saboda kullum girma take yi kuma irin girman da ake so ba lalacewa ba. Duk wanda ya san kungiyar nan a baya ya santa a inda take a can baya, wato […]
Aminiya: Me za ka bayyana mana a kan irin halin da wannan kungiya take ciki?
Daura: Alhamdulillahi! Wannan kungiya tana cikin hali mai kyau, saboda kullum girma take yi kuma irin girman da ake so ba lalacewa ba. Duk wanda ya san kungiyar nan a baya ya santa a inda take a can baya, wato ofishinta dake can kusa da Gwangwan. To kullum cigaba ake so saboda haka lura da cewa ma’aikatanta suna da yawa wannan wuri ya yi mana kadan. To bayan mun ba masu wancan wuri hakuri da kuma gaya musu irin halin da muka samu kanmu na karuwar mutane, shi ne dalilin da yasa muka taso daga wancan ofis muka dawo nan, inda ka same mu saboda ya fi can isasshen wuri.
Anan muna da ofisoshi kamar biyar wadanda anan din ma sai da muka dan gama ofisoshin wuri daya. Muna da ofishin Sakatare, Ma’aji, ofishin gudanarwa na mulki sai kuma ofishin shugaba. Amma saboda sanin cewa duk abinda kake yi saboda Allah to Allah Zai yi maka jagora, sai ya zamo shugabanninmu suna kula da mu fiye da yadda muke zato. Duk lokacin da hakkinmu ya zo a wata wato Fansho suna ba mu. To fanshon nan in yazo kamar yadda hukuma tace a rarraba a fitar da kason da za a kai wuraren da aka ce a kai, to in an kawo na ofis muka yi ‘yan abubuwan da zamu yi, to dan abinda ya rage shi ne muka yi asusu muna ajiyewa. To a kwana a tashi har sai da muka ga asusunmu da nauyi. To ganin haka sai na ce yana da kyau a samu wani abu a kafa kungiyar nan yadda zata zauna dindindin. Karshe dai muka samu fili a bisa hanyar Jibiya muka saya domin gina matsugunni, kuma har an fara aikin gina ofis din, saboda dukkan inda muka zauna a matsayin haya muke zama. Ka ga anan sai muce an samu ci gaba. A da daga shugaba sai sakatare sai masinja sune ke ta gudanar da ayyukan ofis din, to amma yanzu an samu sassa a kalla kamar biyar wadanda kowanne sashe da irin aikin da yake gudanarwa, nan ma ka ga wani cigaba ne. Karin wani cigaban ma da muke shirin aiwatarwa anan gaba kadan shi ne na sayo na’ura mai kwakwalwa mu sanya domin ci gaba da ayyukanmu tare kuma da tafiya da zamani.
Aminiya: Akwai wani ci gaba ko tallafin da za a ce ‘ya’yan kungiyar sun samu?
Daura: Farko dai ita wannan kungiya tamu ta son juna ce. Duk abinda ya samu daya daga cikinmu ya samu kowa. Kazalika, bamu da karami ko babba, duk wanda ya rubuto mana cewa ga wani abinda ya same shi na farin ciki ko akasi, to zamu yi kokari mu tallafa mashi da dan wani abu ta hannun wakillan da zamu tura don taya murna ko jajen abinda ya same shi. Kuma wannan abu muna yinsa a duk inda wani dan fansho yake a cikin jahar Katsina, sai dai in bai rubuto ba, to ka ga anan babu abinda zamu iya yi domin bamu sani ba.
Aminiya: To a sauran wasu wuraren fa? Misali a ce fayil ya bace na dan fansho ko wata matsalar daban.
Daura: Anan bamu da wata matsala domin ka ga dattijon nan da yake gabana, Alhaji Abdu Dutsinma, ina tabbatar maka da cewa duk wani lungu ko sako da aka ce wani fayil ya makale, to sai ya je ya lalabo shi ya fiddo.
Aminiya: Kungiyarku kowa na kallonta a matsayin kungiyar dattawa kuma tsaffin ma’aikata, amma kuma hakan bai hana ta samun ‘yan korafe-korafe ba a tsakanin juna, ko me zaka ce?
Daura: To ka san an ce ‘hada kai karfi ne’ to yadda kanmu ya hadu gaba daya bamu da wata matsala mai karfi irin wannan. Koda an samu wanda ya fita, to mun san zai dawo domin duk zagayen da zai yi ba zai samu yadda yake so ba kamar yadda za a yi masa a kungiyance. Kuma mu anan matakin jaha duk wani abinda ya gagaremu to mu kan tafi a matakin kasa wanda kuma cikin dan karamin lokaci sai aga an samu biyan bukata. Lallai ba za a ce bamu da tsogwami ba baki daya, saboda yawan da muke da shi kuma kowa akwai daga inda ya fito a wajen aiki, to kuwa dole a samu kuka iri-iri tamkar wanda ya ajiye garken dabbobi daban-dabam, in ya ji kukan akuya sai ya ji na tunkiya ko saniya da sauransu. Amma da ka fadi wancan take kace mu tsaffi ne, to ai mu kamata ya yi ita gwamnati ma ta sanya mu gaba mu yi mata jagora. Ku yi kaza kada ku yi kaza domin mu ma haka muka yi muka gama lafiya. Ka ga ni nan saida na yi shekara 35 ina aiki, kuma yanzu shekara ta 20 da ajiyewa, ashe kenan ina da damar in yi aiki ko in fadi yadda za a yi aiki. To shi aiki duka in ka sanya shi cikin jama’a sai ka ja damara da hakuri. Ina jawo hankalin wadanda teburansu suke a yanzu kafin su zo inda muke su rika hakuri da abokan aikinsu.
Aminiya: Shin kungiyarku ta wadanda suka yi aiki a matakin jaha, kananan hukumomi ce ko har da na gwamnatin tarayya?
Daura: Kungiyarmu ta kunshi duka wadannan sassan muddin ka taba sanya hannu a wajen karbar albashi, kuma aka wayi gari ka ajiye aikin kuma an baka dan hakkinka to kana cikin wannan kungiyar.
Aminiya: Mene ne dangantakar wannan kungiya da gwamnati a halin yanzu?
Daura: Na ji dadin wannan tambaya domin kuwa wannan gwamnati ta jaha ta iske mu kusan tsirara. Subhanallahi! Wato abin da ya sa nace haka shi ne, muna da daruruwan mutane ko dubbai wadanda suke neman hakkinsu na shekara daya har zuwa uku ko ma fi, amma ba su samu ba. Rigunan jikinsu sun fara cirewa, idan ka sanya hannu a tsakanin kwalar riga da wuyan mutun sai hannunka ya shige. An kai halin La haula sai Allah ya kawo wannan gwamnati ta Aminu Bello Masari. A lokacin da muka je wajensa domin kai kokenmu sai ya ce, “Ai dama mun yi da ku in har Allah Ya sa na ci, domin ni ma mai karbar fansho ne a gidanku nike ba kuma zan bari gidanmu ya lalace ba, don haka mene ne matsalarku?”
Muka sanya hannu muka baje masa ita, ya ce insha Allahu indai ina bisa wannan kujerar zan bi daya bayan daya domin yi gaba daya sai Allah. Kun san na yi wa jama’a alkawurra iri-iri saboda haka ku cigaba da hakuri zan rika bin abin a hankali har sai na ga na cika dukkan alkawuran da na dauka. Mun ga dil, domin da labarin kashi 33 muke ji amma sai ga shi ya fara da shi, duk mai karbar fansho ya shaida haka. Daga nan sai ya nufi biyan kudin sallama ga wadanda ba a biya na tsawon shekarun can da na fadi domin har wasu ma sai dai aka ba marayun da suka bari domin har suka mutu ba a biya su wancan hakkin ba. Anan abin da nike so jama’a su fahimta akan sha’anin aikin gwamnati musamman ta fuskar biyan wasu kudi shi ne, komin gwamnati take son biyanka kudin kuma ga su a hannu, to da zarar an samu faruwar wani abu wanda ya fi naka muhimmanci to za a karkatar da kudin zuwa can sai daga baya ta biya ka, sai dai kuma ba a daukar dogon lokaci don ba ka wancan hakkin. Saboda haka ina kira ga wadanda aka tantance ba a biya su ba da su yi hakuri, wannan nike fadin haka a matsayina na shugaba ba wai gwamna ko gwamnati ba, cewa in Allah Ya so nan ba da dadewa ba za a biya su.
Aminiya: Shin ina batun tsarin kashi 18 cikin 100 na albashi wanda wannan karin ya shafe ku?
Daura: To wancan da aka ce karancin albashi dubu 18 a lokacin da gwamnatin tarayya ta fadi haka daga cikin jihohin nan sai da aka samu wasu gwamnonin da sai da suka yi tamkar su dauki gora su ce ina na ga kudi? A hannu daya kuma wani gwamnan yana da kudin amma kuma in ya ba da zai koma baya. A karshe dai a wancan lokacin sai su gwamnonin suka hadu domin sanin abin da za su yi. To a takaice dai har yanzu wasu jihohin ba su san da wannan karancin albashi na dubu 18 ba balle ma su biya. Amma mu anan jahar Katsina Allah Ya sa an yi bakin gwargwado sai dai mu masu karbar fansho ance duk lokacin da aka yiwa ma’aikata kari to muma a tunkuda mu domin mu rika ganin wadanda ke gabanmu. Wannan kuma na daga cikin abubuwan da zamu sake tunkarar gwamna da su.
Aminiya:A iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu a tsakaninku da wannan gwamanti ta Masari?
Daura: Kwalliya tana bisa hanyar biyan kudin sabulun domin da zarar Gwamna ya biya mu, to zamu sa riga mai asake da leshi-leshi mu je mu yi masa godiya kuma mu nuna masa yadda ya mayar da mu, kuma mun san hakan zata faru bada dadewa ba da ikon Allah. Wato muna jiran ya iyar da biyanmu bashin da muke bi.
Aminiya: Ko akwai kira ko shawara?
Daura: To da farko ina so in ba ‘yan-uwa wadanda ke can nesa kila ko rediyon jaha ma ba ta zuwa inda suke da su daina amfani da jita-jita. Su rika amfani da ofisoshin kananan hukumomin da suke ciki na kungiya, saboda kwarar ashana daya sai ta toye Katsina kila har da makwabta. Amma yada jita-jita ba shi da wani amfani bayan maganar da za a yada ba ta da wani tushe. Duk abinda gwamnati za ta yi tana aiko mana a rubuce haka mu ma a rubuce muke aikawa. Ga gwamnati kuma, anan ba sai na ce komai ba domin sun sani mu ma mun sani. Sai dai kuma ina so in yi amfani da wannan dama domin mika ta’aziyyarmu ga ‘yan-uwa da abokanmu akan rashin Sakataren wannan kungiya na jaha, Alhaji Amadu Danmalam. Gaskiya kungiya ta yi babban rashi. Allah ya jikan musulmi baki daya. Na gode.