Muna neman masu daukar nauyin zanga-zanga ruwa a jallo —Gwamnati

Hukumar ta kuma ƙara sanya ido domin hana shigowar ‘yan ƙasashen waje zuwa cikin ƙasar.

Muna neman masu daukar nauyin zanga-zanga ruwa a jallo —Gwamnati

Gwamnatin Najeriya ta sanar da neman mutanen da ke daukar nauyin zanga-zangar adawa da kuncin rayuwa a kasar daga ketare ruwa a jallo.

Hukumomin tsaro musamman  Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa sun sanya masu ɗaukar nauyin zanga-zangar a cikin jerin mutanen da suke sa ido kansu.

Kwanturola-Janar ta Hukumar, Kemi Nandap, wacce ta bayyana hakan a hedikwatar tsaro da ke Abuja ranar Talata, ta ce za a kama waɗannan mutanen da ke ƙasashen waje nan take idan suka taka ƙafafunsu a Najeriya.

Ta bayyana hakan ne jim kaɗan bayan wani muhimmin taro da babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya kira.

A baya dai Aminiya ta ruwaito cewa babban hafsan tsaro da sauran shugabannin hukumomin leƙen asiri da na soji suna tattaunawar sirri da nufin aiwatar umarnin murƙushe zanga-zangar da Shugaba Bola Tinubu ya bayar.

Nandap ta ce, “Akwai masu ɗaukar nauyin zanga-zangar ’yan ƙasashen waje, suna cikin jerin sunayen mutanen da muke bibiya.

“Da zarar sun yi yunƙurin shigowa ƙasar na, za a sanar da mu kuma za a kama su a miƙa su ga hukumar da ta dace.”

Ta ce, hukumar ta tura ƙarin jami’ai zuwa kan iyakokin ƙasa da filayen jiragen sama don tabbatar da harkokin shige da fice a kan iyakokin ƙasar yadda ya kamata.

A cewarta, hukumar ta kuma ƙara sanya ido domin hana shigowar ’yan ƙasashen waje zuwa cikin ƙasar.

A nasa ɓangaren, Darakta]Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Yusuf Bichi, ya ce hukumar ta bankaɗo wasu masu ɗaukar nauyin zanga-zangar amma ya ƙi bayar da ƙarin bayani.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS