Gwamnati na tuhumar Lamido Sanusi da tallafa wa Boko Haram

Gwamnatin Tarayya ta zargi dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi da samar da kudi ga aikace-aikacen kungiyar Boko Haram.Lauyan da ke kare gwamnatin a karar da Lamido Sanusi ya kai gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, Fabian Ajagu ne ya yi wannan zargi a takardar martanin da ya gabatar gaban […]

Gwamnati na tuhumar Lamido Sanusi da tallafa wa Boko Haram

Gwamnatin Tarayya ta zargi dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi da samar da kudi ga aikace-aikacen kungiyar Boko Haram.
Lauyan da ke kare gwamnatin a karar da Lamido Sanusi ya kai gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, Fabian Ajagu ne ya yi wannan zargi a takardar martanin da ya gabatar gaban kotun.
Lamido Sanusi yana karar gwamnatin ne kan kwace masa fasfo da kuma keta masa hakkinsa na dan Adam, inda ya bukaci kotun ta haramta wa jami’an hukumar tsaron kasa (SSS) da ’yan sanda daga kama shi.
A ranar Litinin da ta gabata ne lauyan Lamido Sanusi Mista Kola Awodehin ya bara kan wannan takardar martani, inda ya shaida wa kotun cewa, gwamnatin ta kirkiro wannan karya ne bayan ta kwace fasfo din.
Awodein  ya ce, “kwace fasfon wanda yake karewa da wadanda ake kara na uku suka yi ya keta ’yancinsa na tafiye-tafiye . Wanda ake karana farko zuwa na uku sun bayar da dalilai masu karo da juna kan zargin da suke yi wa mai kara: Wannan karo da juna ya nuna sun yi abin da suka yi ne ba tare da bin doka ba.”
Ya kara da cewa: “zargin da ake yi wa mai kara na bayar da kudin gudanar da ayyukan ta’addanci kirkirar karya ce ta wadanda ake karar wadda ba wata hujja a kai, domin babu wani zargin kirki da ke nuna mai kara ya aikata wani laifi. Domin doka ta nuna balo-balo yadda za a gudanar da irin wannan aiki, don haka ina rokon Mai shari’a ya yanke hukuncin cewa mai kara bai aikata wani laifi da wadanda ake kara suke zargi ba.”
Alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Buba ya dage yanke hukunci kan wannan takaddama zuwa jiya Alhamis, sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba mu samu bayanin yadda zaman ya kaya ba.
Sanusi dai yana karar Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a Bello Adoke da Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya Mohammed Abubakar da Hukumar SSS inda yake neman kotun ta hana su ko jami’ansu kama shi ba tare da bin doka ba. Kuma ya shigar da karar ce kwana daya bayan dakatar da shi daga mukaminsa.