Gwamnati ta amince da biyan bashin biliyan 26 ga kamfanonin raba wutar lantarki
Majalisar Zartarwar Kasa ta amince da biyan bashin Naira biliyan 25 da digo tara da kamfanonin raba wutar lantarki ke binta. Ministan Wuta da Aiki da Gidaje, Babatunde Raji Fashola shi ne ya yi furucin yayin da yake yi wa manema labaran fadar shugaban kasa karin bayani jim kadan bayan taron majalisar kasa wanda Shugaba […]

Majalisar Zartarwar Kasa ta amince da biyan bashin Naira biliyan 25 da digo tara da kamfanonin raba wutar lantarki ke binta.
Ministan Wuta da Aiki da Gidaje, Babatunde Raji Fashola shi ne ya yi furucin yayin da yake yi wa manema labaran fadar shugaban kasa karin bayani jim kadan bayan taron majalisar kasa wanda Shugaba Buhari ya jagoranta jiya.
Bashin kudin ya samo asali ne sakamakon wutar lantarkin da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya suka zuka.
Fashola ya ce tun lokacin da gwamnati ta hau kan karagal mulki basussukan da kamfanonin raba wutar lantarki ke bin gwamnati ya zama abin damuwa.