Gwamnati ta ba da hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba da Alhamis na wannan makon a matsayin ranakun hutun Kirsimeti.

Gwamnati ta ba da hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara

Kyautar Kirsimeti

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba da Alhamis na wannan makon a matsayin ranakun hutun Kirsimeti.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta fitar a safiyar Litinin ta kuma ayyana Laraba,` 1 ga watan Janairu, 2025 a matsayin ranar hutun Sabuwar Shekara.

Ministan ma’aikatar, Olubunmi Tunji-Ojo ta hannun Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya buƙaci ’yan Najeriya su yi amfani da damar wannan lokaci wajen wanzar da zaman lafiya da sadar da zumunci da cigaban ƙasa.

Ya kuma jaddada ƙoƙarin Gwamnati wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasar.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa