Gwamnati ta ba da hutun Maulidi
An ba da hutun don murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta.
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata 19 ga watan Oktoban 2021, a matsayin ranar hutu domin bikin maulidi da tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W).
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Shu’aib Belgore.
Sanarwar ta ruwaito Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola yana taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyeyyen halitta.
Ya gargadi dukkan ’yan Najeriya da su zama masu hakuri da juriya tare da koyi da kyawawan dabi’u na Annabi, yana mai cewa yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.
Aregbesola ya umarci ’yan Najeriya musamman Musulmai, da su guji tashin hankali sannan su rika su yi hannun riga da aikata miyagun laifuka.
Kazalika, ya yi kira da a kaucewa aikata abubuwan da za su kawo rarrabuwar kai a tsakanin al’ummar kasar nan.
Ministan ya bukaci dukkan ’yan Najeriya da musamman matasa, da su rungumi dabi’un aiki tukuru da kauracewa zaman kashe wando.
Ya jadadda cewar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba za ta gushe ba wajen ci gaba da hada kan daukacin ‘yan kasa baki daya.