Gwamnati ta bai wa Direbobin Danfo wa’adin daina kasuwanci a kan gadojin Legas
Gwamnatin ta ce Direbobin Danfo na janyo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa a kan gadoji.
Gwamnatin Legas ta sanar da bai wa direbobin bas wa’adin kwanaki bakwai da su daina kasuwancinsu a saman gadojin da ke jihar.
Mashawarci na musamman ga Gwamnan Jihar Legas kan Harkokin Sufuri, Sola Giwa, ya ce ‘Izinin tashin’ ya ta’allaka ne a kan buƙatar kawar da duk wani abu da ke kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa a kan gadoji a fadin jihar.
- Kasashen Larabawa sun bukaci sojojin Isra’ila su fice daga Gaza
- Ana zargin matar aure da satar mazakuta a Abuja
Ya ce duk da gargaɗin da aka yi, direbobin motocin bas na kasuwanci da aka fi sani da ‘Direbobin Danfo’ na ci gaba da bijire wa umarnin gwamnati tare da haifar da cikas sosai a kewayen wadannan gadoji.
Jami’in ya ce gwamnati ta gina tashohin mota da gareji domin gudanar da harkokin kasuwanci a jihar.
Giwa ya ƙara da cewa, “Hukumar za ta fara aiwatar da tsauraran matakan tsaro nan da nan bayan wa’adin ya ƙare.”
Ya kuma ce ayyukan waɗannan direbobin bas na kasuwanci a kan gadoji ya saɓa wa tanadin dokar sake fasalin fannin sufurin jihar Legas na 2018 da aka yi wa kwaskwarima.
Ya ce bayan cikar wa’adin za a gurfanar da waɗanda suka karya dokar gaban kuliya.